'Dan Takaran APC Ya Raba wa Mutane Kudi, Ya Batar da Miliyoyi a Tashi Guda a Kaduna
- Samaila Abdu Sulaiman ya kaddamar da rabon tallafin kudi ga musamman mata da marasa karfi
- ‘Dan siyasar ya fara rabon ne a mazabarsa ta Unguwan Sarki a karamar hukumar Kaduna ta Arewa
- Dujjiman Zazzau ya kashe miliyoyi a kan mata da dattawa sama da 300 kuma ya ce za a fadada shirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Hon. Samaila Abdu Sulaiman ya kaddamar da wani shirin tallafi da ya kawo domin mutanen yankinsa su tsaya da kafafunsu.
Samaila Abdu Sulaiman wanda yake rike da sarautar Dujjiman Zazzau ya dauko wannan aiki ne lokacin da ake shirin fara kamfe na 2027.

Source: Facebook
Dujiman Zazzau ya yi rabon tallafi a Kaduna
Jaridar Legit Hausa ta samu labarin rabon da aka yi ne a wani da ya fitar kuma ya aiko mata.
A farkon makon nan tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayyan ya raba kudi ga marasa karfi a mazabar Kaduna ta Arewa da ke jihar Kaduna.
Makasudin rabon tallafin shi ne a ji kan marasa galihu, a taimaka wa gidaje, sannan a samar da hanyoyin da jama’a za su rike kan su.
An soma rabon a Unguwan Sarki inda aka ce mutane 316 sun amfana da tallafin kudi domin mutanen mazabar su yi kananan kasuwanci.
Kudin zai taimaka wajen karfafa kasuwanci ko kuma a fara kananan sana’o’in da za su ba magidanta damar daukar dawainiyar yau da gobe.
Mutane sun samu N20, 000 zuwa N50, 000
Da yake jawabi wajen rabon, Hon. Samaila Abdu Sulaiman ya tabbatar da cewa da gaske yake yi wajen taimakon kowa a mazabarsa.
Dujima ya ce ya yi hakan ne domin jama’a musamman mata, matasa da sauran marasa karfi da dama su sharbi romon damukaradiyya.
Wani na kusa da ‘dan siyasar ya bayyana a shafinsa cewa mutanen da aka zaba sun tashi da N20, 000 zuwa N50, 000 a rabon da aka fara yi.
A cewarsa a lokaci guda ya kashe Naira miliyan 15 domin ya taimaki masu kananan sana’o’in. Legit ba ta samu bayanin kudin da aka batar ba.
Babangida Agaie ya daura bidiyon ‘dan siyasar a shafin Facebook yana cewa ya saba ba mutanensa taimako irin wannan a shekarun baya.
Hadimin na gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce a wasu lokutan da ya raba kudi irin haka, amma ba a tsaya daukar labarin tallafin ba.
“Yau rana ce da mu ke kara bada tallafi duba da yanayi. Dama lokaci-lokaci muna yin wannan abin.
"Kuma kamar yadda ka ke gani, wannan ba na biyu ba ne, idan ka ce na takwas, ka yi daidai."
- Samaila Abdu Sulaiman
Mata 250 da maza 66 sun samu tallafi
Shugaban kwamitin yakin neman zaben 'dan siyasar, Al-Ameen Murtala Dabo ya ce an taimaka wa mata 250 da kuma maza 66 da kudi.
Wasu wadanda taimakon ya isa kan su sun nuna farin cikinsu, tare da yi wa Dujima addu’ar samun nasara ya koma Majalisar wakilai.
'Dan majalisar Kaduna ya bar APC
An ji lokacin da ɗan majalisar wakilai daga jihar Kaduna, Samaila Suleiman, ya murabus daga jam'iyyar APC saboda zargin rabuwar kai.

Kara karanta wannan
Sojoji da jiragen yaƙi sun zafafa hare hare, sun rutsa yan bindiga ta sama da ƙasa a jihohi 2
Sannan, Dujjiman Zazzau din bai bayyana takamaiman sabuwar jam'iyyar siyasar da yake shirin komawa ba a cikin wasikar murabus dinsa.
Tsohon ɗan majalisar dokokin tarayyan ya aike da wasikar murabus ɗinsa ga shugabannin APC da unguwa da karamar hukumar da ya fito.
Asali: Legit.ng

