Karshen Alewa: EFCC Ta Cafke Ɗan China, An Faɗi Manyan Laifuffukan da Ya Aikata

Karshen Alewa: EFCC Ta Cafke Ɗan China, An Faɗi Manyan Laifuffukan da Ya Aikata

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da wani ɗan China, Li Kuang Kuang a gaban kotu a Legas bisa zargin ta'addanci da damfara ta yanar gizo
  • An kama Li Kuang Kuang a samamen da EFCC ta kai masu damfarar intanet a Legas a 2024, kuma yau kotu ta bayar da ajiyarsa a gidan yari
  • A wani ci gaban, wata kotu a Jos ta yanke wa wasu 'yan China huɗu hukuncin ɗaurin shekaru biyar ko tara saboda hakar ma'adinai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Hukumar EFCC a Legas ta gurfanar da wani dan China, Li Kuang Kuang, a gaban Mai shari’a Daniel Osiagor na babbar kotun tarayya da ke Ikoyi, a ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025.

Wanda ake zargin na daga cikin mutane 792 da EFCC ta kama a ranar 19 ga Disamba, 2024, a yayin wani samame da aka yi a Legas kan damfarar kudi ta intanet da kuma damfarar soyayya.

EFCC ta gurfanar da dan China kan ta'addanci ta intanet yayin da aka daure wasu 4 shekara biyar
Li Kuang Kuang, dan China da EFCC ta kama yana damfara ta intanet a Legas. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

EFCC ta gurfanar da dan China kan 'ta'addanci'

An gurfanar da Li Kuang Kuang bisa tuhumar aikata laifin ta’addanci da damfara ta yanar gizo, kamar yadda EFCC ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takardar tuhumar ta ce:

“Kai Li Kuang Kuang da kamfanin Genting International Co. Limited, wani lokaci a watan Disamba 2024, a Legas, kun yi amfani da na'urar kwamfuta wajen hargitsa tattalin arzikin Najeriya da zamantakewar al’umma."

EFCC ta ce wannan laifi ne da ya saba da sashe na 18 na dokar hana laifuffukan intanet ta 2015, wadda aka sabunta a 2024, yayin da Li Kuang Kuang ya musanta aikata laifin.

Kotu ta tura dan kasar China gidan yari

Lauyan masu kara, U.S Kyari, ya roki kotu da ta tsaida ranar da za a fara shari’a tare da bayar da ajiyar wanda ake tuhuma zuwa gidan gyaran hali.

Mai shari’a Osiagor ya umarci a mika Kuang zuwa gidan gyaran hali da ke Ikoyi, sannan ya dage cigaban sauraron karar zuwa 18 ga Yuli, 2025.

A wani ci gaba kuma, Mai shari’a Dorcas V. Agishi na babbar kotun tarayya da ke Jos, jihar Filato, ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 ga wasu 'yan China hudu bisa laifin hakar ma’adinai ba bisa doka ba.

Kotu ta daure wasu 'yan china shekara 5

EFCC ta sanar a shafinta na X cewa wadanda aka yankewa hukuncin su ne Liang Quin Yong, Wang Huajie, Zhong Jiajing da Long Kechong.

An kama su ne a ranar 8 ga Maris, 2025 a wurin hakar ma’adinai na kamfanin JLM Mining, bisa sahihan bayanan sirri da EFCC ta samu.

An gurfanar da kowane daga cikinsu da tuhumar hakar ma’adinai ba tare da lasisi ba, kamar yadda sanarwar ta nuna.

Hukumar EFCC ta samu nasara a kotu kan wasu 'yan China 4 da ta kama suna hakar ma'adanai a Jos
Ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Abuja. Hoto: @officialEFCC
Asali: Facebook

Dukkaninsu sun amsa laifin da aka karanto musu, inda lauyoyin EFCC, M.O. Arumemi da F.A.I Asemebo, suka bukaci kotu ta yanke hukunci.

Mai shari’a Agishi ta tabbatar da cewa EFCC ta gabatar da hujjojin da ake bukata, don haka ta yanke wa 'yan Chinan hudu hukuncin daurin shekaru 5 ko biyan tarar N1,000,000 kowanne.

Kotun ta kuma bayar da umarnin cewa a kore su daga Najeriya bayan kammala zaman gidan gyaran hali, tare da haramta musu sake shigowa kasar.

Karanta sanarwar EFCC a kasa:

Ana shirin kama dan China kan yaga Naira

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani ɗan ƙasar China ya yi wulakanta kuɗin Najeriya a gaban jami'an hukumar LASTMA a jihar Legas saboda an rufe kamfaninsa.

Wani faifan bidiyo da ya yadu ya nuna ɗan Chinan yana yayyaga takardun N1,000 cikin fushi, lamarin da ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta.

Kakakin rundunar a Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ya bukaci jami'ansu a jihar Lagos su kaddamar da bincike kan lamarin tare da cafko wanda ake zargi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.