Sanatocin PDP 4 da Suka Koma APC a Mulkin Shugaba Tinubu

Sanatocin PDP 4 da Suka Koma APC a Mulkin Shugaba Tinubu

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC na ƙara yawan mambobinta a majalisar dattawa sakamakon ficewar da wasu sanatocin PDP suka yi.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Sanatocin waɗanda suka yi murabus daga PDP, sun koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Sanatocin PDP sun koma APC
Adamu Aliero, Ned Nwoko sun koma APC bayan ficewa daga PDP Hoto: Shamsu Aliero, Senator Ned Nwoko, Armiyau Shuaibu
Asali: Facebook

Sanatocin PDP sun koma APC a mulkin Tinubu

Tun bayan hawan mulkin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, sanatocin jam'iyyar PDP akalla guda huɗu ne suka koma jam'iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatocin sun bayyana mabambantan dalilai waɗanda suka sanya su sauya sheƙa daga PDP wacce suka lashe zaɓe a ƙarƙashinta a shekarar 2023.

Da yawa daga cikinsu suna ba da dalilin cewa rikicin da ya addabi jam'iyyar ne ya sanya suka sauya sheƙa zuwa APC.

1. Ned Nwoko

Sanata Ned Nwoko
Sanata Ned Nwoko ya tsallaka daga PDP zuwa APC Hoto: Senator Ned Nwoko
Asali: UGC

Sanata Ned Nwoko mai wakiltar Delta ta Arewa shi ne sanatan PDP da ya fara komawa APC a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Nwoko ya yi nuni da cewa rarrabuwar kawuna a cikin PDP shi ne babban dalilin da ya sanya ya fice daga jam'iyyar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Sanatan ya sanar da ficewarsa daga PDP ne a cikin wata wasiƙa da aikawa shugaban PDP na mazaɓa ta 8 a ƙaramar hukumar Aniocha ta Arewa.

2. Sanata Adamu Aliero

Sanata Adamu Aliero
Sanata Adamu Aliero ya fice daga PDP zuwa APC Hoto: Shamsu Aliero
Asali: Facebook

Sanata Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC a wata wasiƙa da ya aikawa shugaban majalisar dattawa.

Tsohon gwamnan na jihar Kebbi ya bayyana cewa sauya jam’iyyar da ya yi ya biyo bayan tunani mai zurfi, shawarwari, da kuma nazarin matsalolin siyasar Najeriya da buƙatun mazabarsa.

“Na yanke shawarar fita daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar APC, wacce ina daga cikin waɗanda suka kafa ta."
"Wannan shawara ba ta zo da sauƙi ba. Na kasance mamba mai alfahari da PDP, jam’iyyar da ta ba ni damar yin takara da kuma wakiltar mutane na."

“Amma dai siyasa ba wai ta sadaukar da kai ga jam’iyya kadai ba ce, ya kamata siyasa ta kasance hidima, mafita, da kuma sakamako ga al’umma."
"A yau, na ɗauki wannan mataki ne saboda tambaya guda ɗaya da kowanne shugaba mai kishin kasa yake yi wa kansa, menene abin da ya fi dacewa ga mutanen da nake wakilta?
"A cikin watanni da suka gabata, ya bayyana a fili a gare ni cewa PDP a halin da take ciki yanzu ta rabu da muradun ƴan Najeriya da take cewa tana son jagoranta."

3. Sanata Yahaya Abdullahi

Sanata Yahaya Abdullahi
Sanata Yahaya Abdullahi ya koma APC bayan ficewa daga PDP Hoto: Senator Yahaya Abdullahi
Asali: Facebook

Sanata Yahaya Abdullahi wanda ke wakiltar Kebbi ta Arewa ya yi murabus daga jam'iyyar PDP tare da komawa APC mai mulki a Najeriya.

Tsohon shugaban masu rinjayen na majalisar dattawa ya bayyana komawarsa jam’iyyar APC a matsayin dawowa gida, tun bayan barin jam’iyyar a 2022 saboda rikicin siyasa a jiharsa, cewar rahoton Premium Times.

"A tuna cewa a ranar 14 ga watan Yuni, 2022, na fice daga jam’iyyar APC tare da yin murabus daga matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa ta tara sakamakon saɓani na siyasa a jihata.

“Ina farin cikin sanar da cewa wadannan sabani yanzu an warware su yadda ya kamata ƙarƙashin gwamnatin gwamnan yanzu."
“Saboda haka, babu wani dalili da zai hana ni komawa APC, musamman ganin cewa ni na kasance daya daga cikin waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar da kuma nasarorinta. A gare ni, komawa APC kamar dawowa gida ne."
"Haka kuma, yana da muhimmanci a siyasa cewa na haɗe da shugaban ƙasa, Bola Tinubu."

- Sanata Yahaya Abdullahi

4. Sanata Garba Mai Doki

Sanata Garba Mai Doki
Sanata Garba Mai Doki ya fice daga PDP zuwa APC Hoto: Armiyau Shuaibu
Asali: Facebook

Sanata Garba Mai Doki mai wakiltar Kebbi ta Kudu, yana daga cikin sanatocin jam'iyyar PDP da suka koma APC mai mulki.

Jaridar The Punch ta ce Sanata Garba Maidoki ya bayyana cewa rashin tsaro a mazabarsa da rikicin cikin gida a PDP sune manyan dalilan sauya jam’iyyar da ya yi.

"Wannan mataki zai ba ni damar shiga cikin shirin sabon fata da aka sanya domin amfanin mazaɓata da Najeriya gaba ɗaya."

“Tun lokacin da na kama aiki a matsayin sanata a watan Yuni 2023, fiye da ƙauyuka 100 a mazabata sun kasance ƙarƙashin ƴan bindiga, inda jama’a ke fama da tsoro na garkuwa da mutane, fyaɗe da kuma satar dabbobi."
"Da taimakon Allah, tura sojoji zuwa wasu sassan mazaɓata ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsaro a yankin, kuma mafi yawan jama’ata sun koma gida suna noman su cikin lumana."

- Sanata Garba Mai Doki

PDP ta yi martani kan ficewar sanatocinta

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Kebbi ta yi martani kan ficewar sanatocinta zuwa abokin hamayyarta ta APC.

Jam'iyyar ta bayyana cewa ba ta damu da ficewar sanatocin ba domin hakan ba zai mata tasiri da ƙarfin da take da shi a jihar ba.

Hakazalika ta kuma zargi sanatocin da cin amanarta bayan ta ba su mafaka lokacin da APC ta hana su tikitin yin takara a zaɓen 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng