Zaben 2027: Akpabio Ya Fadi Lokacin Rugujewar PDP da Sauran Jam'iyyu

Zaben 2027: Akpabio Ya Fadi Lokacin Rugujewar PDP da Sauran Jam'iyyu

  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya taso tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP a gaba
  • Godswill Akpabio ya bayyana cewa PDP ta tarwatse kuma ba ta wani ƙarfi a siyasance a jihar Akwa Ibom
  • Shugaban majalisar ya kuma nuna cewa zuwa nan da shekarar 2027, babu wata jam'iyyar siyasa da za a samu a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Akwa Ibom - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ba ta da wani ƙarfi na siyasa a jihar Akwa Ibom.

Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa alamar jam’iyyar wato “laima” yanzu ta yage ta tarwatse, kuma ba za ta iya kare mutane ba.

Godswill Akpabio
Godswill Akpabio ya ce PDP ta tarwatse Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron bayar da tallafi da aka gudanar a filin wasa na Ikot Ekpene a ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio ya yi hasashen rugujewar jam'iyyu

Akpabio ya yi hasashen cewa babu wata jam’iyyar siyasa da za ta kasance a jihar nan da zaɓen 2027.

Ya bayyana cewa dukkan jam’iyyu za su haɗe ne domin marawa ƴan takara ƙalilan baya, ba tare da la’akari da jam’iyyunsu ba, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

"Yayin da nake magana da ku yanzu, babu wani abu da ake kira jam’iyyar siyasa a jihar Akwa Ibom nan da shekarar 2027."
"Dangane da kujerar Sanata Ikot Ekpene, dukkan jam’iyyu sun haɗe domin kaɗa ƙuri’a ga Sanata Godswill Akpabio. Haka kuma, domin kujerar gwamnan jiha a 2027, dukkan jam’iyyu sun haɗe domin kaɗa ƙuri’a ga Gwamna Umo Eno."
"Jam’iyyar PDP ta tarwatse, kuma yanzu laima ba zai iya ba da kariya ba."

- Sanata Godswill Akpabio

Godswill Akpabio ya yabi Gwamna Eno

Sanata Akpabio, wanda ke wakiltar mazaɓar Sanatan Arewa-Maso-Yammacin Akwa Ibom, ya yabawa Gwamna Eno da cewa mutum ne mai son zaman lafiya kuma mai tsoron Allah na haƙiƙa.

Godswill Akpabio
Akpabio ya ce yanzu laimar PDP ba ta ba da kariya Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook
“Umo Eno mai tsoron Allah ne. Ba na magana a kan waɗanda kawai suke ambaton Allah da baƙi. Ina magana ne a kan waɗanda suka sanya Allah a zuciyarsu. Umo Eno ya haɗa mu gaba ɗaya."

- Godswill Akpabio

A wajen taron, Akpabio ya rabawa ƴan mazaɓarsa 1,690 tallafin kayayyaki ciki har da ƙananan motocin haya, keke Napep, injinan sarrafa rogo, janareto, murhunan girki da buhunan shinkafa.

Haka kuma ya sanar da cewa za a ƙaddamar da ayyukan mazaɓa guda 68 tsakanin ranakun 16 da 17 ga watan Mayun 2025.

Sanatocin PDP da suka koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu daga cikin sanatocin jam'iyyar PDP sun koma APC a mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanatoci dai guda huɗu ne suka sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki tun bayan da aka yi zaɓen shekarar 2023.

Dukkanin sanatocin sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan dalilansu na yin hijira daga PDP zuwa APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng