Manyan Labarai A Yau
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ya ce ta ki yi wa 'yan Najeriya aiki.
Wasu mahara sun kai hari kan bayin Allah a jihar Plateau. Miyagun maharan sun hallaka mutum hudu ciki har da wani jariri mai watanni 9 a duniya a yayin harin.
Kamfanin sufurim jiragen sama na Air India ya tabbatar da cewa jirginsa da ya tashi daga birnin Ahmedabad zuwa London Gatwick ya gamu da mummunan hatsari.
Wasu daga cikin jihohin Najeriya sun ba da tallafi ga Alhazansu da ke kasa mai tsarki. An ba da tallafin ne domin saukakawa Alhazan yayin gudanar da aikin Hajji.
Wani malami a jami'ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa a jihar Jigawa, Dr Zaidu Jibril ya lashe kyautar fassara ta duniya ta Sarki Abdallah bin Abdulaziz a Saudiyya
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ba zai ce ba zai yo takara ba da shugaban kasa Bola Tinubu ba a zaben 2027. Ya ce ya shirya shiga hadaka.
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar tsohuwar jakadar Najeriya a ƙasashen ketare guda biyu, Ambasada Ibironke Adefope ta riga mu gidan gaskiya a jihar Oyo.
Wata kotun majistire ta yanke hukuncin zaman gidan kaso na tsawon watanni 13 ga wasu manyan ƴan TikTok ko zaɓin tara kan laifin yaɗa hotunan banza a midiya.
Tsohon ministan sufuri a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ya shirya yin hadaka don kalubalantar Bola Tinubu a 2027.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari