Goodluck Jonathan Ya Shirya Sake Takara a Zaben 2027? An Ji Gaskiya
- An yaɗa wani saƙo mai nuna cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan na shirin tsayawa takara a 2027
- Tsohon shugaban ƙasan ya fito ya yi magana kan wannan saƙon wanda aka yaɗa a manhajar Instagram
- Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ba da yawunsa aka fitar da wannan saƙon ba, hasalima ko kaɗan bai san da shi ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya yi magana kan batun sake tsayawa takara a zaɓen 2027.
Goodluck Jonathan ya nesanta kansa daga wani saƙo da aka wallafa a manhajar Instagram wanda ke nuna cewa yana shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa saƙon an sanya shi ne a wani shafi na manhajar Instagram mai ɗauke da sunan Goodluck Jonathan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yaɗa jita-jita kan Jonathan
Wannan saƙon, wanda aka wallafa daga wani shafi da ke ɗauke da sunan Jonathan, ya soki shugabannin Najeriya na yanzu.
Saƙon da aka wallafa ya zarge su da “yin kamar suna barci”, tare da kiran ƴan ƙasa da su zaɓi shugabanci na gari a shekarar 2027.
“Tun da shugabanninmu na yanzu suna yin kamar suna barci, muna roƙon Allah ya dawo mana da shugabanci na gari a 2027, zaɓin ku ne zai tantance kyautatuwar makomar mu."
- A cewar saƙon
Saƙon yana haɗe da kiɗa da wani hoto wanda ake zargin na kirkirar AI ne, da ke nuna Jonathan yana gaisawa da shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump.
Tun bayan yin wannan wallafar, sama da mutum 16,000 suka duba saƙon, yayin da mutum 1,261 suka yi tsokaci a kansa.
Me Jonathan ya ce kan yin takara a 2027?
Sai dai, yayin da jaridar TheCable ta tuntuɓi mai magana da yawun Jonathan, Ikechukwu Eze, a ranar Juma’a, ya ƙaryata wannan saƙo.
Ikechukwu Eze ya bayyana cewa saƙon tsantsagwaron ƙarya ce kuma tsohon shugaban ƙasan ba shi da shafi a manhajar Instagram.
“Tsohon shugaban Ƙasa Jonathan ba shi da shafi a Instagram."
- Ikechukwu Eze

Asali: Getty Images
An sha danganta Jonathan da yin takara
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da Jonathan ke nesanta kansa daga wasu lamuran siyasa da ake danganta masa.
A gabanin zaɓen shekarar 2023, Jonathan ya ƙi karɓar fom ɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa da wata ƙungiya mai goyon bayansa ta siya a madadinsa.
Jonathan ya nesanta kansa da fom ɗin da aka siya masa don yin takara ne a cikin wata sanarwa da masu kula da harkokin yaɗa labaransa suka fitar a wancan lokacin.
"Ba shi da masaniya a kan wannan yunƙuri kuma bai ba da izinin hakan ba.".
- A cewar sanarwar
Bello El-Rufai ya nemi afuwar Jonathan
A wani labarin kuma, kun ji cewa Bello El-Rufai ya fito ya nemi afuwar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.
Bello El-Rufai wanda ɗa ne a wajen tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nemi afuwar Jonathan ne kan sukar da ya yi masa lokacin da yake shugabancin Najeriya.
Ɗan majalisar mai wakiltar Kaduna ta Arewa ya bayyana cewa rashin wayau ne ya sanya ya caccaki Jonathan a wancan lokacin.
Asali: Legit.ng