Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana cewa matakan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka, sun taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa za su tabbatar da cewa an kirga kuri'un da aka kada musu a zaben 2027.
Tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed ya sake yin kalamai masu kaushi kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan jihar Borno, Faresa Babagana Umara Zulum, ya ba da tallafin kudi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Neja. Ya jajantawa gwamnati.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, shawara kan ayyukan da yake yi a babban birnin na Najeriya.
Jam'iyyar APC a jihar Rivers ta aika da sakon gargadi ga Gwamna Siminalayi Fubara. Ta bayyana cewa dole ya nemi sulhu na gaskiya idan yana son ya tsira daga tsigewa.
Hon. Aminu DanHamidu, shugaban karamar hukumar Bindawa a jihar Katsina, ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Gwamnati da al’umma sun yi jimamin wannan rashi.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ba da tallafin kudi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a jihar Neja. Ya kuma ba da kwnagilar ayyuka.
Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Legas ta samu koma baya bayan manyan jiga-jiganta sun sauya sheka zuwa APC mai mulki. Sun bayyana cewa jam'iyyar ta mutu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari