Tsohon Ministan Buhari Ya Tabo Batun Yin Takara da Tinubu a Zaben 2027
- Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya taɓo batun yin takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen shekarar 2027
- Rotimi Amaechi ya bayyana cewa bai cire yiwuwar fafatawa da Tinubu a zaɓen 2027 domin neman shugabancin Najeriya
- Hakazalika, tsohon ministan ya bayyana shirinsa na shiga haɗakar ƴan adawa domin ƙalubalantar Shugaba Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon ministan sufuri a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan yin takara da Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa bai cire yiwuwar fafatawa da Shugaba Tinubu ba a babban zaɓen shekarar 2027.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amaechi ya yi magana kan takara da Tinubu
Amaechi, wanda ya zo na biyu a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC wanda ya samar da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a 2022, ya ce bai cire yiwuwar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 ba, yana mai cewa lokaci ne zai nuna hakan.
Wannan bayani na Amaechi na zuwa ne ƙasa da wata guda bayan shugabannin APC sun amince da Tinubu a matsayin ɗan takara guda ɗaya na jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Shugabannin adawa da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da wasu da dama, suna ƙoƙarin kafa haɗaka don kifar da Tinubu a 2027.
Sai dai, Amaechi ya jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar APC, amma ya ce kasancewarsa mamba a jam’iyya mai mulki ba yana nufin dole ne ya goyi bayan gwamnati ko da tana yin abin da yake ba daidai ba, cewar rahoton Vanguard.
Ko da yake ya ce a halin yanzu ba ya shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa, ya ƙara da cewa hakan abu ne mai yiwuwa, domin yana ganin har yanzu yana da abin da zai iya bayarwa.
Rotimi Amaechi zai shiga haɗakar adawa
Hakazalika Amaechi ya bayyana shirinsa na haɗa kai da jam’iyyun adawa domin ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027, yana mai nuna damuwarsa kan matsin tattalin arziki da ke ƙara tsananta a ƙasar nan.

Asali: Facebook
Amaechi ya bayyana cewa yana tattaunawa da wasu ƴan Najeriya masu kishin ƙasa waɗanda ke ganin ana tafiyar da ƙasar nan ba daidai ba, domin su haɗa kai su dunƙule waje ɗaya.
“Muna tunanin cewa idan muka haɗu muka yi nasara a zaɓe, ƙasar nan tabbas za ta samu sauyi."
"Na daɗe ina faɗin cewa Boko Haram ba rikicin addini ba ne. Yawancin mutanen da ke ciki na yi ne saboda raɗaɗin talauci da yunwa."
- Rotimi Amaechi
Shugaba Tinubu ya taya Amaechi murna
A wani labarin kuma, kun ji cewa Bola Tinubu ya aika da saƙon taya murna ga tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
Shugaban kasa Tinubu ya aika da saƙon ne domin taya tsohon gwamnan na jihar Rivers murnar cikarsa shekara 60 a duniya.
Mai girma Bola Tinubu ya bayyana Amaechi a matsayin ɗan siyasa na ƙwarai wanda ya hidimtawa jihar Rivers da Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng