An Zo wajen: Tinubu Ya Tsage Gaskiya kan Shirin Maida Najeriya Karkashin Jam'iyya 1

An Zo wajen: Tinubu Ya Tsage Gaskiya kan Shirin Maida Najeriya Karkashin Jam'iyya 1

  • Shugaban ƙasa ya kwantar da hankulan ƴan adawa masu fargabar za a maida Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya
  • Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa bai da shirin ganin Najeriya ta koma kan wannan tsarin a lokacin mulkinsa
  • Sai dai shugaban ƙasan ya nuna cewa ba za su ƙulle ƙifa ga duk wani ɗan adawa da yake son shigowa jam'iyyar APC ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan batun maida Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya.

Shugaba Tinubu ya kawar da yiwuwar Najeriya ta zama ƙarƙashin jam'iyya ɗaya a lokacin mulkinsa.

Tinubu ya yi magana kan tsarin jam'iyya 1 a Najeriya
Tinubu ya ce Najeriya ba za ta koma karkashin jam'iyya 1 ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a zauren majalisar tarayya a ranar Alhamis a Abuja, a bikin ranar Dimokuraɗiyya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce duk da haka, ba zai ba jam’iyyun adawa shawara su daidaita lamuransu ba.

Jam’iyyun adawa irin su PDP, LP da NNPP sun zargi jam’iyyar APC da shirin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.

'Yan hamayya dai sun fuskanci yawan sauya sheƙa daga ƴaƴansu cikin makonnin da suka wuce.

"Ya fi kyau mu ga jam’iyyun adawa a hargitse."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya kuma ce APC za ta aikata kuskuren siyasa ne idan ta hana ƴan jam’iyyun adawa da ke sauya sheƙa shiga cikinta, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Me Tinubu ya ce tsarin jam'iyya ɗaya?

“Ga waɗanda ke tsoron cewa APC na ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙarƙashin jam’iyya ɗaya, ina ba ku alƙawari na ƙashin kaina. Yayin da maganganunku na iya zama sakamakon firgita, kun yi kuskure."
“A ko da yaushe, a baya, a yanzu, ko nan gaba, ba zan taɓa ɗaukar ra’ayin ƙasa mai jam’iyya ɗaya a matsayin abu mai kyau ga Najeriya ba. Ba na ƙoƙarin sauya rajistar kowace jam’iyya a hukumar INEC."

"Haka kuma, abokaina, ba za mu iya zargin wanda ke ƙoƙarin tserewa daga jirgin da ke nutsewa ba, ko da ba shi da jakar ceto."
“Najeriya ba za ta zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba. Wannan ba zai faru ba. Amma za mu aikata kuskuren siyasa ne idan muka rufe ƙofofi ga masu shigowa APC.”
"Muna maraba da masu son shigowa APC. Kada a rufe ƙofa ga kowa. Jam’iyyun da ke jin tsoron rasa ƴaƴansu, abin da ya fi shi ne su binciki tsarin cikin gida da harkokinsu maimakon ɓullo da abin da babu shi."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan adawa
Tinubu ya ce suna maraba da masu son shigowa APC Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya yi kuskure a jawabinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kuskure a jawabin da ya yi na ranar dimokuraɗiyya.

A cikin jawabin da ya yi, Shugaba Tinubu ya lissafa sunayen fitattun mutane biyu; Pa Reuben Fasoranti da Dr. Edwin Madunagu, cikin jerin matattun da aka karrama, alhalin suna nan a raye ba su mutu ba

Fadar shugaban ƙasa ta fito ta ba da haƙurin kan wannan akasin da aka samu, inda ta ce an yi kuskuren ne ba da gangan ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng