Amaechi: Tafiyarsu Atiku Ta Samu Karuwa, Tsohon Ministan Buhari Ya Shirya Shiga Hadaka
- Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya taɓo batun shiga haɗakar jam'iyyun adawa don ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a 2027
- Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ya shirya shiga haɗaka da wasu ƴan siyasa waɗanda ke ganin abubuwa ba su tafiya daidai
- 'Dan siyasar wanda ya yi gwamna a Ribas ya kuma koka da cewa ana fama da matsananciyar yunwa a ƙasar domin shi kansa yana jin ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan shirin shiga haɗakar ƴan adawa da Atiku Abubakar ke jagoranta.
Rotomi Amaechi ya bayyana shirinsa na shiga haɗaka don ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Amaechi, wanda babban jigo ne a jam'iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rotimi Amaechi ya shirya shiga haɗaka
Amaechi ya nuna damuwarsa kan halin da ƙasar nan ke ciki, tare da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin kafa haɗakar siyasa da za ta iya kawo canji na gaskiya.
Ya ce ko da yake bai kammala yanke shawarar tsayawa takarar shugaban ƙasa ba, lokaci ne kawai zai nuna ko zai shiga takara a 2027, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Sai dai Amaechi ya jaddada cewa yana nan daram cikin jam’iyyar APC, amma hakan ba yana nufin goyon bayan gwamnati ko da tana tafiya ba daidai ba.
“Idan gwamnati ta gaza wajen kawo ci gaba a ƙasa, ba za ka ce kawai ka bi ta saboda kuna cikin jam’iyya ɗaya ba. Ka san hakan ba daidai ba ne."
- Rotimi Amaechi
Amaechi ya ce abin da ya dace shi ne a faɗa wa gwamnati gaskiya tare da bayyana abin da ƴan ƙasa ke bukata.
Ya koka kan yawaitar yunwa da talauci a ƙasar nan, inda ya ba da misalin yadda ya ga gawar wani mutum a gefen hanya, lamarin da ya danganta da matsanancin rashin abinci.
"Mutane na mutuwa. Mutane na fama da yunwa. Ni kaina ina jin tasirin yunwa."
- Rotimi Amaechi
Amaechi ya yi magana kan yin takara a 2027
Ko da yake ya ce yanzu bai da niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa, Amaechi ya ƙara da cewa hakan zai iya yiwuwa a nan gaba domin yana ganin har yanzu yana da abin da zai iya bayarwa.

Asali: Facebook
"Lalle, ina ganin zan iya bada gudunmawa mai ma’ana."
- Rotimi Amaechi
Amaechi ya bayyana cewa yana tattaunawa da wasu ƴan Najeriya masu kishin ƙasa waɗanda ke ganin al'amura ba su tafiya daidai, domin su dunƙule waje ɗaya wajen kawo sauyi a Najeriya.
Amaechi ya caccaki shugaban INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya caccaki shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu.
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa da a ce shugaban INEC na yanzu ne a shekarar 2015, da ba a yi wa jam'iyyar APC rajista ba.
Tsohon ministan ya kuma zargi shugaban na hukumar INEC da nuna ɓangaranci da son kai tun kafin zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng