Jerin Tarurrukan APC da Tinubu wadanda Buhari Ya Ki Halarta da Dalilansa

Jerin Tarurrukan APC da Tinubu wadanda Buhari Ya Ki Halarta da Dalilansa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC sun gudanar da wasu muhimman tarurrukka a kwanakin baya, wanda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai halarta ba
  • Tsohon shugaban ƙasa Buhari ya bayyana wasu dalilai kan rashin halartar wasu daga cikin waɗannan tarurrukan, yayin da bai ce komai ba kan wasu
  • Dangantaka ta siyasa tsakanin Tinubu da Buhari ta samo asali tun kafin zaɓen 2015, lokacin da suka haɗa kai suka kafa jam’iyyar APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari sun sha bayyana kansu a matsayin abokan siyasa.

Tinubu ya samu yabo a fili wajen taka muhimmiyar rawa da ta taimaka wa Buhari samun nasara a matsayin shugaban ƙasa a 2015, bayan haɗin gwiwar su da ya haifar da kafuwar jam’iyyar APC.

Buhari bai halarci waru tarurrukan APC ba
Ba a ga Buhari a wajen wasu tarurrukan da suka shafi Tinubu da APC Hoto: @OfficialABAT, @Mbuhari
Asali: Twitter

Buhari ya miƙa mulki ga Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, wanda daga nan ya karɓi ragamar shugabancin ƙasa da kuma jam’iyyar APC gaba ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ana cewa ƙarƙashin shugabancin Tinubu, APC ta ware wasu ɓangarori na jam’iyyar.

Duk da Buhari da Tinubu na ci gaba da cewa babu wata matsala a tsakaninsu kuma suna biyayya ga jam’iyyar APC, tsohon shugaban ƙasar ya kasance baya halartar wasu muhimman tarurrukan jam’iyyar ko na gwamnati inda Tinubu ke halarta.

Ga jerin wasu daga cikin waɗannan tarurrukan:

1. Ƙaddamar da littafin IBB

Shugaba Bola Tinubu da dukkan wasu tsofaffin shugabannin ƙasa sun halarci ƙaddamar da littafin tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a Abuja ranar 20 ga Fabrairu, 2025, sai dai Buhari bai je ba.

Maimakon haka, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ne ya wakilce shi, wanda kuma yana daga cikin masu duba littafin.

Jonathan Vatsa, wani jigo a jam’iyyar APC daga jihar Neja, ya bayyana cewa rashin halartar Buhari ba ya rasa nasaba da ƙin jin daɗin juyin mulkin 1985 da aka yi masa.

2. Taron ƙusoshin jam’iyyar APC

Tsohon shugaban ƙasa Buhari da mataimakinsa sun kasance ba su halarci taron farko na manyan ƙusoshin jam’iyyar APC ba.

An gudanar da taron ne a sakatariyar jam’iyyar APC da ke Abuja a ranar Laraba, 26 ga watan Fabrairun 2025.

Mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasan bai samu gayyata kan taro a kan lokaci ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Hakazalika kuma yana da wasu muhimman abubuwa a gabansa a lokacin da aka gudanar da taron.

Buhari ya ki zuwa wasu tarurrukan APC
Ba a ga Buhari a wasu tarurrukan jam'iyyar APC ba Hoto: @DOlusegun, @Mbuhari
Asali: Twitter

3. Buhari bai je Katsina tarbar Tinubu ba

Shugaba Tinubu ya kai ziyara ta kwanaki biyu zuwa jihar Katsina, jihar da Buhari ya fito, ranar Juma’a, 2 ga watan Mayun 2025.

Yayin ziyarar, Shugaba Tinubu ya yaba da tarbar da aka yi masa, sai dai ya bayyana cewa ya yi kewar rashin ganin Buhari a yayin ziyarar da ya kai jiharsa, tare da fatan alheri gare shi.

4. Buhari bai halarci taron ƙolin APC ba

Kamar sauran tarurrukan, tsohon shugaban ƙasan bai halarci taron ƙoli na jam’iyyar APC ba wanda aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 22 ga watan Mayun 2025

Babu wani dalili a fili da aka bayar dangane da rashin halartar Buhari a wajen taron.

A yayin taron, gwamnoni na jam’iyyar APC sun mara wa Shugaba Tinubu baya kan tazarce a 2027, haka nan shugabannin majalisar tarayya ma sun goyi bayan hakan.

5. Taron kammala gasar karatun Alƙur’ani

Buhari ya nuna nadamar rashin iya halartar taron ƙarshe na gasar karatun Alƙur’ani wanda aka shirya a matsayin girmamawa ga marigayiya Alhaja Abibatu Mogaji Tinubu, mahaifiyar shugaban ƙasa Tinubu.

Wannan taro na addini mai muhimmanci, wanda aka shirya ranar Asabar, 31 ga Mayu, 2025, an gudanar da shi ne ƙarƙashin jagorancin Sanata Basheer Lado, CON, kuma an yi tsammanin halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban na Najeriya.

6. Buhari bai halarci taron ECOWAS ba

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bai samu halartar taron bikin cika shekara 50 da kafa ƙungiyar ECOWAS ba.

Buhari ya bayyana cewa rashin halartarsa wajen bikin da aka gudanar a Legas, ya faru ne sakamakon zuwa duba lafiyarsa da yaje yi a Birtaniya, cewar rahoton jaridar Vanguard.

A cikin wata wasiƙa da ya aika wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Buhari ya taya ƙungiyar ECOWAS murna bisa cika shekara 50, tare da bayyana rashin jindaɗinsa na rashin halartar taron.

Ya yabawa ci gaban da ECOWAS ta samu cikin shekaru 50 da suka gabata, tare da amincewa da irin juriyar da ƙungiyar ta nuna duk da ƙalubalen da ta fuskanta.

Buhari ya aika saƙo ga Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya aika da saƙo ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Muhammadu Buhari ya taya shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara biyu a kan karagar mulki.

Tsohon shugaban ƙasan ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da marawa gwamnatin Shugaba Tinubu baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng