Yadda ake Samun Lamunin Kudin Tinubu domin Gina Gidaje
- Bankin Ba da Lamunin Gidaje na Tarayya (FMBN) na bai wa ‘yan Najeriya da suka cancanta damar samun lamunin gidaje ta Asusun Gidaje na Ƙasa (NHF)
- Wadanda suka yi rajista da NHF za su iya samun lamuni har Naira miliyan 50, da kudin ruwa na kashi 6 cikin 100 a shekara, tare da damar biyan bashin har na tsawon shekaru 30
- Za a iya amfani da lamunin wajen sayen gida, gina shi, inganta shi ko gyara shi, amma sai an cika wasu sharuda kafin amincewa da neman bashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Bankin Ba da Lamunin Gidaje na Tarayya (FMBN) ya bayyana yadda ‘yan Najeriya za su iya neman lamunin gidaje domin saye, ginawa, ingantawa ko gyara gidajensu.
Lamunin na Asusun Gidaje na Ƙasa (NHF) yana ba masu bayar da gudunmawa damar samun kuɗin jinginar gida ta hannun Bankunan Jinginar Gida (PMBs) da FMBN ta amince da su.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa bankin ya ce wadanda suka cancanta za su iya samun lamuni har Naira miliyan 50, gwargwadon abin da za su iya biya da kuma darajar gidan da ake son jinginarwa.
Mene ne lamunin FMBN?
Lamunin NHF wata hanyar samun kuɗin gidaje ce da FMBN ke gudanarwa ta hannun Bankunan Jinginar Gida (PMBs) da aka ba lasisi.
Ana iya amfani da kuɗin wajen sayen gida, gina sabon gida, inganta shi ko yin gyare-gyare a gidan da mai neman yake zaune.
Gidan da aka yi amfani da kuɗin wajen saye ko gina shi ne zai zama jinginar da za a yi amfani da ita wajen tabbatar da lamunin.
Su waye suka cancanta?
FMBN ta tanadi wasu sharuda da mai neman lamunin NHF ya kamata ya cika.
Daga cikin sharuddan akwai:
- Ya kasance ɗan Najeriya mai shekaru 18 ko sama da haka.
- Ya kasance mai bayar da gudunmawa ga Asusun Gidaje na Ƙasa (NHF).
- Ya kasance yana biyan gudunmawar NHF ba tare da katsewa ba na akalla watanni shida.
- Ya kasance yana da tabbataccen hanyar samun kuɗin shiga.
- Masu sana’ar kansu su gabatar da shaidar samun kuɗin shiga akai-akai.
- Ya nemi lamunin ta hannun Bankin Jinginar Gida da FMBN ta amince da shi.
- Gidan da za a yi wa jingina ya cika sharudan doka da na tsare-tsaren gine-gine.
Nawa za a ba mutum?
Vanguard ta wallafa cewa shafin FMBN na NHF ya nuna cewa mai bayar da gudunmawa zai iya samun lamuni har Naira miliyan 50.
Sai dai adadin da mutum zai samu zai dogara da ikon biyan bashinsa da sauran sharudan lamunin.
FMBN ta kuma bayyana cewa mutum ba zai samu fiye da kashi 90 cikin 100 na kuɗin ko darajar gidan da ake jinginarwa ba.
Wasu tsofaffin takardun FMBN da bayanai a wasu shafuka har yanzu suna ambaton Naira miliyan 15 a matsayin iyakar lamunin. Sai dai bayanin da ke kan shafin FMBN na yanzu ya nuna Naira miliyan 50.
Saboda haka, masu neman lamunin ya kamata su tabbatar da sabbin sharuddan kai tsaye daga FMBN ko cibiyar jinginar gida da aka amince da ita.

Source: Facebook
Masu bayar da gudunmawar NHF ba za su biya kudin ruwa da ya wuce kashi 6 cikin 100 a shekara ba.
Rahotanni sun nuna cewa wanda zai ci gajiyar lamunin na iya samun damar biyan bashin a tsawon shekaru 30 sannu a hankali.
Yadda ake neman lamunin
Mai neman lamunin zai gabatar da takardun da ake bukata ga Bankin Jinginar Gida ko wata cibiyar bayar da lamunin gidaje da FMBN ta amince da ita.
Bayan an tabbatar da cewa mai neman ya cika sharudan, kuma an amince da lamunin, za a bayar da kuɗin ta hannun cibiyar da aka samo lamunin domin amfani da shi wajen samar gidaje da aka amince da ita.
Ana son fahimtar nasarorin Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani jigo a jam'iyyar APC, Dr Femi Alabi, ya yi gargadin cewa rashin isasshen bayani ga jama'a kan shirye-shiryen gwamnatin Bola Tinubu.
Alabi ya bayyana hakan ne a Abuja yayin ƙaddamar da masu kula da harkokin Tinubu/Shettima a wani tarin masu ruwa da tsaki da aka yi a Abuja.
Ya ce matsalolin tattalin arziki da kuma rashin ingantaccen sadarwa na iya hana ganin nasarorin da gwamnatin ta samu, yana mai kira ga jama'a da su ƙara fahimtar shirye-shiryen gwamnati.
Asali: Legit.ng


