Manyan Labarai A Yau
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi alhinin rasuwar ɗan Majalisa mai wakiltar mazabar Kaura Namoda ta Kudu, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji.
Gobara a kasuwar Gandun Albasa ta kone shaguna hudu a Kano. Asara ta kai miliyoyin naira, amma an dakile bazuwar wutar. An samu ceto a wasu shaguna.
An samu barkewar mummunan fada a tsakanin wasu 'yan bindiga masu gaba da junansu a jihar Kaduna. Rikicin ya yi sanadiyyar kashe miyagun 'ƴan bindiga guda 10.
Wani magidanci, Abubakar Aminu ya kashe dan uwansa Sani Yusuf a Zariya, yayin da a Agwara, wasu mutum shida suka kashe wani Alhassan bisa zargin satar waya.
Sanata mai wakiltar Borno ta Tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Kaka Shehu Lawan, ya yi wa ministan yada labarai, martani kan matsalar rashin tsaro.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi ya nuna damuwa kan yadda abubuwa suka tabarbare a Najeriya. Ya ce mutane na kara talaucewa a kullum.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi gyara a jihar Kebbi. Ruwan saman ya yi sanadiyyar rugujewar gidaje sama da 200. Gwamna Nasir Idris zai ba da tallafi.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar babban jigon jam'iyyar APGA, Maja Umeh ranar Laraba, 9 ga watan Afrilu, 2025, ya mutu yana da shekara 64 a duniya.
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kaddamar da yakin neman sake zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a babban zaben 2027. Ya ce sun shirya tsaf.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari