Bayan zuwa Kaduna, Uba Sani Ya Tabo Batun Barazanar da Tinubu zai Fuskanta a 2027
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan haɗakar ƴan adawa da ke son gani bayan Bola Tinubu a zaɓen 2027
- Sanata Uba Sani ya bayyana cewa shugaban ƙasan bai da wata barazana da zai fuskanta a zaɓen da ake tunkara
- Gwamnan ya kuma soki ƴan adawa kan zargin da suke yi na cewa hukumar INEC ta hana rajistar sababbin jam'iyyu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa babu wata barazana da ke fuskantar Shugaba Bola Tinubu dangane da zaɓen shekarar 2027.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa haɗakar ƴan adawa ba wata barazana da za ta iya kawowa ga shugaban ƙasan.

Asali: Twitter
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a daren ranar Juma’a a cikin shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Gwamna Uba Sani, da yawa daga cikin waɗanda ke ƙoƙarin haɗewa waje ɗaya don su ƙalubalanci gwamnatin yanzu, ba su shiga cikin gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya a ƙasar nan ba.
Uba Sani ya ce Tinubu bai da barazana a 2027
"Zan iya gaya maka a yau, amma ka je ka rubuta kuma ka tuna da wannan ranar, Asiwaju ba shi da wata barazana, kuma zan gaya maka dalilina."
"Ka ga, na gaya maka cewa mafi yawan rayuwata na yi ne a matsayin mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam. Mun yi gwagwarmaya don kafa dimokuraɗiyya a Najeriya, da kuma shugabanci nagari."
"Yawancin mutanen da ke magana a yau, ina suke a lokacin? Lokacin da muke cikin tsaka mai wuya, muna fafutuka don dimokuraɗiyya, adalci, shugabanci nagari, da bin doka, ba su ma san abin da ake ciki ba."
- Gwamna Uba Sani
Gwamna Uba Sani ya soki ƴan adawa
Gwamnan ya kuma tabo zarge-zargen da ke cewa hukumar INEC na hana rajistar sababbin jam’iyyun siyasa, yana mai cewa ƴan adawa kawai suna neman mulki ne.

Asali: Facebook
“Akwai wata hanya ta yin gwagwarmaya. Lokacin da muka yi wannan gwagwarmayar ƙarƙashin jagorancin jagoranmu, Cif Gani Fawehinmi (Allah ya jikansa), kun san me ya faru? Ba mu yi gwagwarmaya don neman mulki ba."
"Mun yi gwagwarmaya ne saboda muna so mu tabbatar da dimokuraɗiyya da shugabanci nagari a Najeriya."
“Shi ya sa lokacin da Abdulsalami Abubakar ya fara shirin miƙa mulki, ka tuna, yana ce cewa jam’iyyun da za a yi rajista uku ne kawai, AD, APP da PDP, muka tafi da tawagarmu, sai jagoranmu Cif Gani Fawehinmi ya ce ba za mu shiga wannan zaɓen ba."
"Sai muka kalle shi muka ce, meyasa? Sai ya ce, saboda fa ba a gama yaƙin ba. Dole ne mu ci gaba da fafutuka domin faɗaɗa tsarin siyasa a Najeriya."
“Kuma wannan ne dalilin da ya sa wasu daga cikinmu, har da ni kaina muka kai INEC kotu."
"Don haka idan mutane na magana kan hana rajista ko makamancin haka, abin mamaki ne a gare ni. Ina suke a wancan lokaci? A shekarar 2000, ko ma tun 1999, mun kai INEC kotu."
- Gwamna Uba Sani
Uba Sani ya caccaki masu sukar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ragargaji masu sukar Shugaba Bola Tinubu.
Uba Sani ya bayyana cewa mafi yawan masu sukar shugaban ƙasan, ba su yi wani abin a zo a gani ba lokacin da suke kan madafun iko.
Gwamnan ya nuna cewa mafi yawan matsalolin da suka addabi ƙasar nan, sun fara ne tun kafin Bola Tinubu ya hau kan mulki.
Asali: Legit.ng