An Jefi Shugaba Tinubu yayin Ziyara a Kaduna? An Ji Yadda Lamarin Ya Kaya

An Jefi Shugaba Tinubu yayin Ziyara a Kaduna? An Ji Yadda Lamarin Ya Kaya

  • An riƙa yaɗa jita-jitar an yi yunƙurin jifar Shugaban kasa Bola Tinubu yayin ziyarar da kai a jihar Kaduna
  • Gwamnatin jihar Kaduna ta fito ta bayyana cewa sam ko kaɗan babu wani abu makamancin hakan da ya faru
  • Ta bayyana cewa mutanen Kaduna sun fito don tarbar Shugaba Tinubu cikin murna da farin ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnatin Kaduna ta ƙaryata jita-jitar da ke cewa an kusa kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu hari a yayin ziyararsa ta baya-bayan nan zuwa jihar.

Gwamnatin ta kuma bayyana gaskiyar abin da ya faru a faifan bidiyon wanda ya karade kafafen sada zumunta.

Gwamnatin Kaduna ta musanta jifar Tinubu
Gwamnatin Kaduna ta ce ba a jefi Tinubi Hoto: @ubasanius, @DOlusegun
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kaduna, Ibraheem Musa ya musanta cewa an jefi shugaban ƙasan a wata hira da aka yi da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yaɗa batun jifar Bola Tinubu a Kaduna

A ranar Alhamis, yayin da Shugaba Tinubu ke jawabi a filin Murtala Square wajen ƙaddamar da wasu ayyuka, wani gajeren bidiyo ya nuna jami’an tsaro suna dakatar da wani mutum da ba a bayyana ko waye ba ya tunkari shugaban ƙasan.

A cikin bidiyon, an ga Shugaba Tinubu ya dakata na ɗan lokaci sannan ya ce cikin natsuwa “Ku bar shi,” kafin ya ci gaba da jawabin nasa.

Bidiyon ya haifar da muhawara sosai a kafafen sada zumunta, inda wasu ke cewa an yi ƙoƙarin jifar shugaban ƙasa da dutse ko kuma an yi yunƙurin kai masa hari.

Gwamnati ta musanta batun jifar Tinubu

Sai dai, Ibraheem Musa, Babban Sakataren yaɗa labarai na Gwamna Uba Sani, ya bayyana cewa babu wani hari ko jifa da aka yi.

Ya bayyana mutumin da ya kusanci dandalin a matsayin wani magoyin baya da ke cikin murna da ƙauna ga shugaban ƙasa.

“Mutanen Kaduna sun tarbi Shugaba Tinubu cikin ƙauna, kuma an yi farin ciki. Matashin da aka gani yana ƙoƙarin nuna ƙaunarsa ce ga shugaban ƙasa."
"Har ma shugaban ƙasa ya ji daɗi, ya ce a bar shi. Wasu kawai suna ƙoƙarin bata sunan mutanen Kaduna ne."

- Ibraheem Musa

Sanya sunan Tinubu ya jawo cece-kuce

Hakazalika cece-kuce ya biyo bayan sauya sunan asibitin ƙwararru da aka ƙaddamar da shi zuwa sunan Shugaba Tinubu, maimakon barin sunan wanda ya fara aikin, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo.

Gwamnatin Kaduna ta ce ba a kai wa Tinubu hari ba
Gwamnatin Kaduna ta kare sanya sunan Tinubu a asibiti Hoto: @ubasanius
Asali: Facebook

Sai dai Ibraheem Musa ya bayyana cewa hakan ba wani abin damuwa ba ne.

"Ko tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya ji daɗin ganin hakan. Dangantakar shugaban ƙasa da gwamna ba ta fara yau ba. Babu wani abu na siyasa a ciki."

- Ibraheem Musa

'Tinubu bai da barazana a 2027' - Uba Sani

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi watsi da haɗakar jam'iyyun adawa.

Uba Sani ya bayyana cewa haɗakar ƴan adawan babu wata barazana da za ts iya yi wa Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Gwamnan ya kuma soki ƴan adawa inda ya ce da yawa daga cikinsu ba su yi fafutukar ganin dimokuraɗiyya ta tabbata a ƙasar nan ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng