'Yan Bindiga Sun Farnaki Kauyuka a Plateau, an Hallaka Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Farnaki Kauyuka a Plateau, an Hallaka Bayin Allah

  • Ƴan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hare-haren ta'addanci a wasu ƙauyukan jihar Plateau
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutane 13 tare da ƙona gidaje a hare-haren da suka kai a ƙananan hukumomin Mangu da Bokkos
  • Wasus daga cikin mutanen da aka kashe, sun rasa ransu ne lokacin da suke tsaka da yin aiki a cikin gonakinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Wasu ƴan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe mutane 13, yawanci yara da tsofaffi, tare da ƙona gidaje a jihar Plateau.

Ƴan bindigan sun hallaka mutanen ne a wani hari da suka kai a ƙauyukan Juwan da Manja da ke ƙananan hukumomin Bokkos da Mangu a jihar Plateau.

'Yan bindiga sun kai hare-hare a Plateau
'Yan bindiga sun yi kashe-kashe a Plateau Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Facebook

Tashar Channels tv ta rahoto cewa harin da ya auku a ƙauyen Juwan, da ke cikin yankin Tangur na ƙaramar hukumar Bokkos, ya faru ne da daren ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Plateau

A yayin harin ƴan bindigan sun kashe mutum 10, yayin da suka jikkata wasu da dama.

A ƙauyen Manja, da ke masarautar Chafem a ƙaramar hukumar Mangu, an kashe mutane uku da yammacin ranar Alhamis.

Mutanen da aka kashe suna aiki ne a gona lokacin da maharan suka zo ba zato ba tsammani suka hallaka su.

Wasu daga cikin mazauna garin sun tsira da raunuka lokacin da jami’an tsaro suka kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa daga waɗanda suka tsere daga harin.

Shugaban ƙaramar hukumar Bokkos, Amalau Samuel, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana harin a matsayin ta’addanci da rashin imani.

"Maharan sun shigo ne cikin dare sannan suka fara kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba. Sun riƙa shiga gida-gida ne, inda suka kasa shiga, sai su ɓalle rufin sama su shiga."
"Mafi yawan waɗanda abin ya shafa tsofaffi ne da yara waɗanda ba su da ƙarfin gudu, yayin da matasa suka samu damar tserewa don ceton rayukansu."

- Amalau Samuel

Ƴan bindiga sun yi kashe-kashe

A wani hari daban da aka kai a Manja, masarautar Chafem a Mangu, maharan sun kashe mutane uku a gonarsu, sannan suka ƙone gidaje fiye da 20 kafin jami’an tsaro su iso.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
'Yan bindiga sun kai hare-hare a Plateau Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Dan majalisar dokokin jihar Plateau mai wakiltar Mangu ta Kudu, Mathew Kwarpo, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

"Ƴan ta’addan sun kutsa cikin mutane inda suka kashe mutane uku kafin jami’an tsaro da matasan gari su fatattake su."
"Daga baya ƴan ta’addan sun sake kawo sabon hari a ranr, inda suka ƙone gidaje sama da 20."

- Mathew Kwarpo

Ƴan bindiga sun kashe manoma

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun farmaki manoma a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma.

Ƴan bindigan sun hallaka manoma aƙalla mutun 20 a harin da suka kai a ƙarmaar hukumar Kankara.

Miyagun sun kuma hallaka wasu bayin Allah mutum uku tare da wani jami'in rundunar tsaron jihar Katsina a harin da suka kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng