Atiku Ya Yi Martani kan Zabar ADA a Matsayin Jam'iyyar Hadaka don Yakar APC
- Hadimin Atiku Abubakar ya musanta cewa ƴan haɗaka sun amince da jam'oyyar ADA a matsayin inda za su koma
- Aɓdul Rasheeth ya bayyana cewa ƴan haɗakar ba su zaɓi jam'iyyar ADA ba, domin har yanzu akwai batutuwan da ba su gama tattake waje a kai ba
- Ya buƙaci jama'a da su ƙara haƙuri domin za a ba da bayani a lokacin da ya dace kan shirin ƴan haɗaka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hadimin Atiku Abubakar ya yi magana kan amincewa da ADA a matsayin jam'iyyar da ƴan haɗaka za su yi amfani da ita.
Hadimin na Atiku ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasan da tawagarsa ba su amince da ADA a matsayin jam'iyyar da su yi amfani da ita ba.

Asali: Twitter
Abdul Rasheeth wanda yake mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Atiku Abubakar ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa har yanzu akwai wasu batutuwa da suke buƙatar warwarewa tsakaninsu da haɗakar.
Ƙungiyar da ake kira Nigeria National Coalition Group (NNCG) ce ta gabatar da bukatar rajistar jam’iyyar ADA a gaban hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) a ranar Juma’a gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Rahotanni sun nuna cewa yiwuwar ficewar Atiku da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, daga jam’iyyar PDP, na ƙara jefa jam’iyyar cikin ruɗani.
Su Atiku ba za su zaɓi ADA ba
A cikin saƙonsa, Abdul Rasheeth ya zargi wasu jaridun Najeriya da cewa suna ƙara taimakawa wajen ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.
"Wata ƙungiya na ƙoƙarin samun rajistar jam’iyya, kamar yadda kowanne dan Najeriya ke da damar hakan, amma dole ne su danganta wannan da haɗaka."
"Ba a amince da ADA a matsayin jam’iyyar haɗaka ba tukuna, kuma a lokacin da ya dace, za a sanar da jama’a kan irin matakan da za a dauka. A yi haƙuri a jira."
- Abdul Rasheeth

Asali: Facebook
Rashin tabbas ya baibaye PDP
Wasu majiyoyi daga cikin PDP sun bayyana damuwa kan yadda matsaloli ke ta ƙara taruwa kan jam’iyyar, musamman dangane da yuwuwar ficewar Atiku, David Mark da tsohon shugaban majalisar wakilai, Aminu Tambuwal.
An ce David Mark ne ya jagoranci taron ƙungiyar NNCG inda aka yanke shawarar neman rajistar ADA a matsayin sabuwar jam’iyya.
Ana fargabar cewa da zarar an ba ADA rajista, yawancin magoya bayan waɗannan manyan ƴan siyasa uku za su fice daga PDP su koma sabuwar jam’iyyar.
Atiku, wanda ya taba neman kujerar shugaban ƙasa a shekarun 1993, 2007, 2011, 2015, 2019 da kuma 2023, yana ci gaba da shiri domin wani sabon yunkuri a zaɓen 2027.
Ministan Tinubu ya ƙalubalanci ƴan haɗaka
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya taso ƴan haɗaka a gaba kan shirin zaɓen 2027.
Festus Keyamo ya bayyana cewa babu wani tasiri da ADA za ta yi a kan jam'iyyar APC a zaɓen 2027 da ake tunkara
Ministan ya nuna cewa haɗakar ta su abin dariya ne, domin babu wata haɗewa da ƴan adawa za su yi, da za ta kai ƙarfin irin wanda aka yi wajen kafa APC.
Asali: Legit.ng