Gwamna Uba Sani Ya Taso Masu Sukar Tinubu a Gaba, Ya Fadi Kuskurensu

Gwamna Uba Sani Ya Taso Masu Sukar Tinubu a Gaba, Ya Fadi Kuskurensu

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya caccaki mutanen da ke sukar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Uba Sani ya nuna cewa mafi yawa daga cikin ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta ba a lokacin Tinubu suka fara ba
  • Gwamnan ya bayyana cewa masu sukar shugaban ƙasan ba su taɓuka komai ba lokacin da suke kan madafun iko

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya soki ƴan adawa masu caccakar Shugaba Bola Tinubu.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa ba su yi wani abin a zo a gani ba wajen magance ƙalubalen da ke fuskantar Najeriya a halin yanzu lokacin da suke kan mulki.

Uba Sani ya caccaki masu sukar Tinubu
Gwamna Uba Sani ya yi wa masu sukar Tinubu wankin babban bargo Hoto: @DOlusegun, @ubasanius
Asali: Twitter

Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata tattaunawa a shirin Politics Today na tashar Channels Tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Uba Sani ya kare Bola Tinubu

A cewarsa, wasu daga cikin matsalolin da ƙasar nan ke fama da su, musamman rashin tsaro, sun samo asali ne tun kafin zuwan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

“Duk mutanen da ke magana a yau suna cikin shugabanci a baya, kuma abubuwa na taɓarɓarewa."
"Matakin talauci a Arewacin Najeriya ya ƙaru daga kusan kaso 50% shekaru 15 da suka wuce zuwa kaso 70% a shekarar 2023, sannan wani zai kalle ni ya ce Tinubu ne ya jawo matsalar? Ai wannan ba gaskiya ba ne."

- Gwamna Uba Sani

Gwamna Uba Sani ya ce a shekarar 2014, ƴan bindiga da sauran nau’o’in matsalolin rashin tsaro ba su yaɗu kamar yanzu ba.

Uba Sani ya nuna yatsa ga ƴan adawa

Sai dai ya ce gazawar gwamnatin jam’iyyar PDP a lokacin ne ya sa matsalolin suka ƙara ƙazancewa.

Uba Sani ya kare Shugaba Bola Tinubu
Gwamna Uba Sani ya soki masu caccakar Tinubu Hoto: @ubasanius
Asali: Facebook
“A shekarar 2014, babu wani abu da ake kira ƴan ta’adda ko ƴan bindiga a Birnin Gwari, Giwa, da wasu sassan Zamfara."
"Abin ya fara ne sosai kusan a shekarar 2015 zuwa 2016. Abin da muka sani kawai a yankin Arewa maso Gabas shi ne Boko Haram kafin shekarar 2014."
“Amma mun zauna, ba mu duba alƙaluman ci gaban tattalin arziƙi. Ba mu duba yadda talauci ke ƙaruwa a Arewacin Najeriya ba. Ba mu duba yadda yaran da ba sa zuwa makaranta ke ƙaruwa ba."
“Waɗannan su ne matsalolin. Ba mu duba matsalolin da ke addabar fannin lafiya ba, kamar yadda mutane ke samun sauƙin zuwa asibiti. Kuma wannan ne ya sa abubuwa suka lalace sosai daga shekarar 2017 zuwa 2019."
“Lokacin da nake majalisar dattawa, kullum idan muka tunkari majalisa, abu na farko da za a fara tunani shi ne ko za a yi shiru na minti ɗaya saboda wani abu ya faru, mutane sun mutu. Wannan shi ne labarin a kullum."

- Gwamna Uba Sani

Idan za a tuna, Muhammadu Buhari ne yake kan mulki a shekarun nan na 2015 da 2015 da gwamnan ya ce an fara samun matsalar 'yan bindiga.

Shugaban majalisa ya yabi Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya yabawa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan ayyukan da ya aiwatar a Kaduna.

Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi muhimman ayyuka domin ci gaban jihar.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa mutanen Kaduna ba su da wani da za su zaɓa face Tinubu a zaɓen shekarar 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng