'Yan Bindiga Sun Yi Barna, Sun Yi Awon Gaba da Babban Alkali
- Wasu ƴan bindiga da ke kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi ta'asa a jihar Bayelsa da ke yankin Kudu maso Kudu
- Ƴan bindigan sun yi awon gaba da ƙarfi da yaji da wani alƙalin babbar kotun jiha a birnin Yenagoa
- Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa tana ƙoƙarin ganin an cafke waɗanda suka aikata laifin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun sace wani alƙalin babbar kotun jiha a Bayelsa.
Ƴan bindigan sun sace mai shari’a E.G. Umokoro ne a birnin Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ce an yi garkuwa da mai shari’a Umokoro, wanda ke zama alƙalin babbar kotun jiha ta 7, da ƙarfe 7:30 na yamma a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sace shi a gaban wani mashahurin gidan cin abinci da ke yankin Ekeki na birnin Yenagoa.
Yadda aka sace babban alƙali a Plateau
Wasu shaidu sun bayyana cewa maharan, waɗanda suka sa baƙaƙen kaya, sun yi ƙoƙarin harbinsa, amma ba su yi nasara ba.
Daga nan sai suka tare shi da wata motar Hilux mai launin fari wadda ba ta da lambar rajista, suka kuma tafi da shi cikin ƙarfi da yaji.
An kuma bar mota baƙa ƙirar Toyota Prado da yake ciki a lokacin harin, a wurin da lamarin ya auku.
A cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an ga yadda wanda aka sacen ke ƙoƙarin ƙwacewa daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da shi.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Musa Muhammad, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya bayyana cewa rundunar ta tura tawagar ƙwararru da kuma jirage marasa matuƙa domin bin sawun maharan tare da kama su.
"Rundunar ta tura tawagar ƙwararru da jirage marasa matuƙa domin bin sawun maharan tare da kama su."
- DSP Musa Muhammad

Asali: Original
Wanene alƙalin da aka sace?
Alƙalin da aka sace, wanda ake yi wa kallon mutum mai ƙima a ɓangaren shari’a na jihar Bayelsa, an ce ya dawo ne daga wani taro kafin a farmake shi.
Mai shari’a Umukoro, tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) a Yenagoa, ya riƙe muƙamai da dama a ɓangaren shari’a na jihar, kuma ya jagoranci shari’un manyan laifuka da dama a baya.
A shekarar 2021, ya yanke wa wani mutum hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari saboda lalata da kuma kashe wata yarinya ƴar shekara biyar a ƙauyen Akede da ke ƙaramar hukumar Sagbama ta jihar.
Ya kuma taɓa jagorantar shari’un da suka shafi rigingimun zaɓe da dama a jihar a baya.
Ƴan bindiga sun kashe tsohon shugaban PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kashe tsohon shugaban jam'iyyar PDP a Benue.
Ƴan bindigan sun kashe tsohon shugaban na PDP ne bayan sun buɗe masa wutaa lokacin da suka farmake shi.
Tsohon shugaban na PDP ne a ƙaramar hukumar Tarka shekara guda bayan sun kashe matarsa.
Asali: Legit.ng