'Yan Bindiga Yi Ta'asa, Sun Hallaka Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP

'Yan Bindiga Yi Ta'asa, Sun Hallaka Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun hallaka tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Miyagun ƴan bindigan sun kai farmakin ne kan shugaban shugaban na PDP a ƙaramar hukumar Tarka a daren ranar Juma'a
  • Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ta fara farautar wanda ake zargi da kitsa kai harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Wasu ƴan bindiga sun kashe tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙaramar hukumar Tarka a jihar Benue, Aondoakaa Yaiyol.

Aondoakaa Yaiyol, kafin ƴan bindigan su kashe shi a daren ranar Juma’a, shi ne kwamandan rundunar mafarauta da masu samar da tsaro a jeji (NHFSS) a ƙaramar hukumar.

'Yan bindiga sun yi barna a Benue
'Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban PDP a Benue Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Sakataren yaɗa labarai na PDP a jihar Benue, Tim Nyior, ya tabbatar da kisan Yaiyol a wata tattaunawa ta waya da jaridar The Punch ta yi da shi a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe tsohon shugaban PDP a Benue

An tattaro cewa an kashe matar marigayin tare da ƙona gidansa a shekarar da ta gabata.

Tim Nyior ya bayyana kisan marigayin a matsayin abin takaici.

"Gaskiya ne cewa mutumin ya taɓa zama shugaban PDP a ƙaramar hukumar Tarka kafin ya zama kwamandan rundunar mafarauta da masu tsaron jeji a yanzu."
"Abin takaici ne, matarsa ta mutu a bara cikin irin wannan hali."

- Tim Nyior

Hakazalika mai ba gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, shawara kan harkokin tsaron cikin gida, Cif Joseph Har, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, yana mai bayyana shi a matsayin "kisan gilla".

"An kashe kwamandan NHFSS, Aondoakaa Yaiyol a wani kisan gilla. Sun zo ne a kan babur suka harbe shi daga kusa sannan suka tsere."
“Bayan sun harbe shi, sai suka fara harbi domin firgita mutane sannan suka tsere a babur, inda wasu motoci guda biyu suke basu kariya, su ma suna harbi domin hana mutane kusantowa."

- Cif Joseph Har

'Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban PDP
'Yan sanda sun fara farautar 'yan bindiga a Benue Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan sanda sun yi bayani kan harin

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Benue, DSP Udeme Edet, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa ana farautar wanda ake zargi, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

“Lamarin ya faru, kuma lokacin da ofishin ƴan sanda na Tarka ya samu rahoton, sai aka tura jami’ai don su kama wanda ake zargi, amma kafin su isa maɓoyarsa ya tsere."

- Udeme Edet

Udeme Edet ya tabbatar da cewa za a kama wanda ake zargi nan ba da jimawa ba.

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hare-haren ta'addanci a wasu ƙauyukan jihar Plateau.

Miyagun ƴan binɗigan sun hallaka mutane 15 a hare-haren da suka kai a ƙauyuka biyu na ƙananan hukumomin Mangu da Bokkos a daren ranar Alhamis.

Ƴan bindigan sun kuma ƙona gidaje da dama bayan sun riƙa bi gida-gida sun hallaka bayin Allah da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng