Uba Sani Ya Yi Allah Wadai da Kisan 'Yan Daurin Aure a Plateau, Ya Sha Alwashi
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya nuna takaicinsa kan kisan gillar da aka yi wa masu zuwa ɗaurin aure ƴan asalin jihar a Plateau
- Uba Sani ya bayyana kisan kiyashin da aka yi wa mutanen a matsayin abin ƙyama kuma na rashin imani
- Hakazalika ya buƙaci gwamnan jihar Plateau da ya tabbatar da cewa an zaƙulo waɗanda suka aikata laifin don su fuskanci hukunci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi magana kin kisan kiyashin da aka yi wa matafiya ƴan asalin jihar a Plateau.
Gwamna Uba Sani ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa mutanen guda 12 a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Asali: Twitter
Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutanen da lamarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ne zuwa ƙaramar hukumar Qua’an Pan domin halartar ɗaurin aure, inda aka kai musu hari aka kashe su a yankin Mangun da ke fama da rikici.
Wasu mutum 11 kuma sun jikkata cikin wannan hari, inda suka samu raunika iri daban-daban.
Me Uba Sani ya ce kan kisan ƴan ɗaurin aure?
Gwamna Uba Sani ya bayyana lamarin a matsayin ɗanyen aiki na ƙiyayya da rashin imani.
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta kama waɗanda suka aikata wannan ta’asa tare da gurfanar da su a gaban kotu.
"Mun karɓi wannan labari na kisan mutum 12 ƴan Jihar Kaduna cike da bakin ciki da kaɗuwa. Wannan lamari abin ƙyama ne. Dole ne a bi sawun waɗanda suka aikata wannan aika-aikar, kuma a hukunta su ba tare da ɓata lokaci ba."
"Kada ayi ƙasa a gwiwa wajen ganin cewa an yi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa an hukunta masu wannan laifin."
- Gwamna Uba Sani
Uba Sani ya buƙaci a yi hukunci
Gwamna Uba Sani ya kuma roƙi gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, da ya ɗauki matakan gaggawa wajen tunkarar matsalar tsaro a jiharsa.
"Ina kira ga mai girma Gwamna Caleb Mutfwang da ya ɗauki alhakin jagorantar duka ayyukan tsaro domin ganin waɗanda suka aikata wannan kisan sun fuskanci hukunci."
"Wannan mummunan lamari ya kamata ya zama wata dama ta sauya salo wajen dakile ayyukan miyagun mutane da ke cin karensu babu babbaka."
- Gwamna Uba Sani

Asali: Facebook
Uba Sani ya ba ƴan Kaduna shawara
Gwamnan ya kuma sha alwashin cewa zai sa ido kai tsaye wajen bin diddigin binciken da kuma matakan da hukumomin tsaro za su ɗauka.
“Wannan hauka dole ta tsaya. Ya isa haka. Dole ne mu aika da saƙo mai ƙarfi cewa ba za a ƙara lamuntar rashin hukunta masu laifi a ko’ina cikin Najeriya ba."
- Gwamna Uba Sani
A ƙarshe, Gwamna Uba Sani ya yi kira ga al’ummar jihar Kaduna da su kwantar da hankalinsu yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ganin an samu adalci ga waɗanda abin ya shafa.
An kashe ƴan uwan ango a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu fusatattun matasa sun hallaka masu zuwa ɗaurin aure daga jihar Plateau.
Daga cikin mutanen da aka hallaka har da ƙanin ango, mahaifinsa da kawunsa bayan matasan sun bankawa motarsu wuta.
Wasu daga cikin mutanen da suka tsira daga harin sun samu raunuka inda ake kula da lafiyarsu a asibiti.
Asali: Legit.ng