Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Kaduna Ya Yi Murabus daga Jam'iyyar APC

Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Kaduna Ya Yi Murabus daga Jam'iyyar APC

  • Jam'iyyar APC ta gamu da koma baya a jihar Kaduna bayan tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kagarko ya yi murabus daga cikinta
  • Hon. Nasara Rabo ya sanar da murabus ɗinsa daga jam'iyyar APC cikin wata wasiƙa da ya fitar a ranar Asabar, 21 ga watan Yunin 2025
  • Tsohon shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa ya yanke wannan shawarar ne saboda wasu dalilai na shi na ƙashin kansa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kagarko a jihar Kaduna, Hon. Nasara Rabo, ya yi murabus daga jam'iyyar APC.

Tsohon shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa wasu dalilai nasa na ƙashin kansa ne suka sa ya yanke wanna shawara.

Jam'iyyar APC ta yi babban rashi a Kaduna
Tsohon shugaban karamar hukuma ya bar APC a Kaduna Hoto: Nasara Rabo
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa tsohon shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar da murabus ɗinsa daga jam'iyyar APC ne a cikin wata wasiƙa da ya fitar a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasara Rabo ya raba gari da jam'iyyar APC

Nasara Rabo ya fara harkar siyasa a matsayin kansila mai wakiltar gundumar Iddah a ƙarƙashin tsohuwar jam’iyyar ACN.

Murabus ɗin nasa na nuna wani muhimmin sauyi a siyasar yankin, duba da yadda ya daɗe yana taka rawa a harkokin siyasa a Kudancin Kaduna.

Yayin da yake tabbatar da murabus ɗin nasa, Nasara Rabo ya ce shawarar da ya yanke ta samo asali ne bayan samun gamsuwa a zuciyarsa kan ya bar jam'iyyar APC.

Sai dai bai bayyana ko yana da niyyar shiga wata jam’iyya ba kafin zaɓen 2027 da ake tunkara.

"Ina sanar da cewa na yanke wannan shawara ne bayan yin dogon nazari da tattaunawa tare da wasu mutane na kusa da ni, kuma bisa dalilai na ƙashin kaina."

- Hon. Nasara Rabo

Majiyoyi daga kusa da tsohon shugaban ƙaramar hukumar sun bayyana cewa wannan mataki ba zai rasa nasaba da sauyin siyasa da ke gudana da kuma rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar APC a matakin ƙaramar hukuma da na jiha ba.

Jam'iyyar APC ta yi rashi a Kaduna

Nasara Rabo ya shugabanci ƙaramar hukumar Kagarko har sau biyu a jere, kuma ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun masu ƙarfafa APC a lokacin da ake kafa ta a jihar Kaduna.

Tsohon shugaban karamar hukuma ya fice daga APC a Kaduna
APC ta yi rashin wani daga cikin jiga-jiganta Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ficewarsa ta ƙara adadin mutanen da suka fice ko suka yi murabus daga jam’iyyar APC a jihar Kaduna, a yayin da ake fuskantar rikice-rikicen cikin gida da kuma shirye-shiryen zaɓen da ke tafe.

Ƙoƙarin da aka yi don jin ta bakin jami’an jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Namadi Sambo ya ƙaryata komawa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa ya koma jam'iyyar APC.

Namadi Sambo ya musanta jita-jitar wacce ke cewa ya sauya sheƙa zuwa APC mai mulki a Kaduna.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya nuna cewa wasu ne kawai da ke ƙoƙarin kawo ruɗani suke yaɗa cewa ya fice daga PDP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng