Tsohon Hadimin Tinubu Ya Gano Hanyar Kayar da Shi a 2027
- Hakeem Baba-Ahmed ya ce ’Yan Najeriya za su kori APC a 2027 idan aka gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci
- Shugaban PRP ya ce kada APC ta ji tsoron jam’iyyun adawa, domin ’yan Najeriya ne ke da ikon yanke hukuncin zabe
- Hakeem Baba-Ahmed ya gargadi ’yan adawa kan kawancen da ba shi da cikakken shirin tafiyar da Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Dr. Hakeem Baba-Ahmed, shugaban jam’iyyar PRP na kasa, ya ce ’yan Najeriya za su kada kuri’ar korar APC daga mulki a zaben 2027 idan aka gudanar da zaben cikin ’yanci da adalci.
Baba-Ahmed ya ce babban abin da ya kamata APC ta damu da shi ba jam’iyyun adawa ba ne, illa ’yan Najeriya, wadanda ke da cikakken ikon tantance sakamakon zabe.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan sauye-sauyen siyasa da dabarun jam’iyyun adawa gabanin babban zaben 2027, a wata hira da DITV/Alheri Radio a Kaduna.

Kara karanta wannan
'Yan Najeriya da dab da rasa damar da aka buɗe musu kan batun kafa 'yan sandan jihohi
’Yan Najeriya ne ke zabe
A cewarsa, ba jam’iyyun siyasa ne ke yanke sakamakon zabe ba, domin masu kada kuri’a ne ke zabar ’yan takara da jam’iyyun da za su yi nasara.
“Sun san cewa idan suka bari aka gudanar da zabe cikin ’yanci da adalci, ’yan Najeriya ba za su zabe su ba. Abin da suke tsoro ke nan,” in ji shi.
Shugaban PRP ya kara da cewa:
“Ba adawar sauran jam’iyyun siyasa ya kamata su ji tsoro ba, illa adawar ’yan Najeriya, saboda jam’iyyun siyasa ba sa kada kuri’a, ’yan Najeriya ne suke kada kuri’a.”
Ya ce APC ta san cewa bai wa ’yan kasa damar zabar shugabanninsu cikin ’yanci na iya zama illa ga jam’iyyar a zaben 2027.
Baba-Ahmed ya gargadi 'yan adawa
Baba-Ahmed ya kuma gargadi ’yan siyasar adawa da kafa kawance kawai domin cire Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga mulki, ba tare da samun cikakken shirin yadda za su tafiyar da kasar ba.
“Mun san akwai mutanen da abin da suke nema kawai shi ne a cire Tinubu domin su yi abin da suke so, ko kuma su maimaita irin manufofin da Tinubu yake aiwatarwa a yanzu. Daga baya kuma su ce an yi kuskure,” In ji shi.
Ya jaddada cewa PRP ba za ta goyi bayan dan siyasa kawai saboda burinsa na zama shugaban kasa ba.
“A cikin PRP, ba za mu amince mu goyi bayan wani mutum kawai saboda yana da burin zama shugaban kasa ba. Ba za mu shiga irin wannan yarjejeniya ba. Dole ne mu fara ganin abin da yake da niyyar yi kafin mu amince,” in ji shi.

Source: Twitter
Hakeem Baba-Ahmed ya soki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara na musamman kan lamuran siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya soki Shugaba Bola Tinubu.
Hakeem Baba-ahmed ya bayyana cewa mawuyacin halin da Najeriya take ciki ya karu fiye da lokacin da Tinubu ya karɓi mulki a shekarar 2023.
Asali: Legit.ng
