Kisan 'Yan Daurin Aure a Plateau Ya Je Kunnen Tinubu, Ya ba da Umarni

Kisan 'Yan Daurin Aure a Plateau Ya Je Kunnen Tinubu, Ya ba da Umarni

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna takaicinsa kan kisan da aka yi wa ƴan ɗaurin aure a Plateau
  • Mai girma Tinubu ya bayyana kisan gillar a matsayin abin ƙyama wanda ba za a amince da shi ba ko kaɗan
  • Shugaban ƙasan ya umarci hukumomin da su tabbatar da cewa sun zaƙulo masu hannu a harin da aka kai kan matafiyan da suka taso daga Kaduna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan kisan gillar da aka yi wa matafiya ƴan ɗaurin aure a Plateau.

Shugaba Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan gillar, inda ya bayyana harin a matsayin abin ƙyama kuma rashin imani wanda ba za a amince da shi ba.

Tinubu ya yi Allah wadai da kashe-kashe a Plateau
Shugaba Tinubu ya yi tir da kisan 'yan daurin aure a Plateau Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin sadarwa da dabaru, Bayo Onanuga ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane umarni Tinubu ya ba da kan harin Plateau?

Shugaba Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da su gaggauta kama waɗanda suka aikata laifin tare da tabbatar da cewa an hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

"Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tir da kisan gillar da aka yi wa matafiya a jihar Plateau, inda ya buƙaci jami’an tsaro da su tabbatar sun kamo waɗanda suka aikata laifin domin su fuskanci hukunci."
"Yayin da yake mayar da martani kan kashe mutane 12 da suka haɗa da mahaifi da ɗan’uwan ango, waɗanda ke kan hanyarsu zuwa ɗaurin aure, Shugaba Tinubu ya bayyana wannan aika-aikar a matsayin abin ƙyama da rashin imani."
“Wadanda aka kashe da kuma wasu da suka jikkata, duk suna tafiya ne daga Zariya, jihar Kaduna, zuwa Jos, jihar Plateau."
"Shugaban ƙasa ya umurci rundunar ƴan sandan Najeriya (NPF) da su hada gwiwa da sauran hukumomin tsaro da na leƙen asiri domin tabbatar da cewa an kama masu hannu a wannan mummunan hari."

“Shugaban ƙasa ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da tabbatar da cewa ba za a bar wannan aikin ta’addanci ba tare da hukunci ba."
"Dole ne gwamnatin jihar Plateau ta ɗauki matakin gaggawa wajen shawo kan aukuwar irin wannan tashin hankali da ta’addanci."
"Dole ne gwamnatin jihar ta haɗa kai da hukumomin tsaro domin gano musabbabin wannan hari na baya-bayan nan, kuma a yi amfani da hakan a matsayin darasi domin kauce wa faruwar irin haka a gaba."
"Shugaban ƙasa ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa, al’umma da gwamnatin jihar Kaduna."

- Bayo Onanuga

Tinubu ya yi magana kan harin Plateau
Tinubu ya umarci a zakulo wadanda suka kashe matafiya a Plateau Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Uba Sani ya yi Allah wadai da harin Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya yi Allah wadai kan kisan da aka yi wa matafiya ƴan jihar a Plateau.

Gwamna Uba Sani ya buƙaci da a tabbatar da cewa an hukunta masu hannu a mummunan harin da suka kan masu zuwa ɗaurin aure.

Ya kuma yi kira ga gwamnan Plateau da ya jagoranci aikin zaƙulo masu hannu a aika-aikar da aka yi kan matafiyan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng