Gwamnatin Kebbi Ta Bada Tallafi bayan Mummunan Harin 'Yan Bindiga
- Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da kisan mutane a wasu munanan hare-hare da ƴan bikdiga suka kai a wasu ƙauyuka
- A yayin hare-haren da ƴan bindigan suka kai, sun hallaka mutane 30 tare da raunata wasu da dama
- Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Tafida ya ziyarci ƙauyukan domin yi musu jaje tare da ba su tallafin kuɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta bayyana ɓarnar da ƴan bindigan suka yi a wani mummunan harin da suka kai.
Gwamnatin ta tabbatar da asarar rayuka 30 sakamakon hare-haren da ƴan bindigan suka kai a wasu ƙauyuka na yankin Zuru.

Asali: Facebook
Tashar Channels tv ta ce shugabannin ƙananan hukumomin Zuru da Danko Wasagu, Muhammad Gajere da Hussaini Bena, suka bayyana hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin sun bayar da rahoton cewa mutane 16 ne suka rasa rayukansu a Tadurga, yayin da wasu 14 suka mutu a Kyebu da Yar-Kuka da ke yankin Waje.
Yayin wata ziyarar da mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Tafida, ya kai Tadurga a ranar Juma’a, Muhammad Gajere da Hussaini Bena sun bayyana cewa akwai mutane da dama da suka jikkata.
Haka kuma, miyagun ƴan bindigan sun tafi da dabbobi da wasu kayayyaki masu daraja.
Gwamnatin Kebbi ta yi jajen harin 'yan bindiga
Sanata Umar Tafida ya isar da ta’aziyyar gwamnatin jihar a yayin ziyarar jajantawa mutanen ƙauyukan da ya kai.
Ya miƙa saƙon gaisuwar ta’aziyya ga mutanen Tadurga da ke cikin ƙaramar hukumar Zuru, da kuma Kyebu da ke cikin ƙaramar hukumar Danko Wasagu, dukkansu a cikin masarautar Zuru.
A madadin Gwamna Nasir Idris, ya tabbatar wa da mazauna yankunan cewa gwamnati na daukar matakan inganta tsaro, kuma za a rufe dukkan hanyoyin shiga garuruwan Tadurga da Kyebu domin hana sake afkuwar irin wannan hari a gaba.
Sanata Tafida ya kuma yi addu’a domin samun rahama ga rayukan waɗanda suka rasa ransu, tare da roƙon Allah Ya ba iyalansu juriyar rashin da suka yi.

Asali: Original
Kebbi: Gwamnatin jihar Kebbi ta bada tallafi
Hakazalika, Sanata Umar Tafida ya sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 50 ga al’ummomin da abin ya shafa, Naira miliyan 25 ga Tadurga da kuma Naira miliyan 25 ga Kyebu.
Ya bayyana wannan tallafin a matsayin ƙoƙarin taimaka wa iyalan da suka rasa ƴan uwansu a wannan lokaci mai wahala.
Ƴan Lakurawa sun takurawa manoma a Kebbi
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan Lakurawa sun taso manoman ƙaramar hukumar Augie ta jihar Kebbi a gaba yayin da suke aike musu da saƙon barazana.
Ƴan ta'addan na Lakurawa sun gargaɗi manoman kada su kuskura su daina amfani da dabbobi wajen gudanar da ayyukan noma a gonakinsu, inda suka ce duk wanda ya yi amfani da injuna za su kashe shi.
Barazanar da ƴan ta'addan suka yi ta haifar da firgici da ruɗani a tsakanin manoman yankin, musamman waɗanda suka rasa dabbobinsu saboda satar shanu da miyagun suka daɗe suna yi musu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng