'Yan Sanda Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Bindiga a Katsina

'Yan Sanda Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Bindiga a Katsina

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari kan manoma da ke tsaka da gudanar da aiki a gonakinsu
  • Jami'an ƴan sanda sun yi gaggawar kai ɗauke zuwa inda lamarin ya auku tare da samun nasarar daƙile harin
  • Ƴan sandan sun samu nasarar daƙile harin tare da ceto manoman da ƴan bindigan suka sace bayan sun farmake su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun samu nasarar daƙile wani harin da ƴan bindiga suka kai.

Jami'an ƴan sandan sun kuma ceto wasu manoma guda shida da aka sace, a harin da ƴan bindigan suka kai a dajin Kwari Manaja da ke cikin ƙaramar hukumar Sabuwa.

'Yan sanda sun samu nasara kan 'yan bindiga
'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun ragargaji ƴan bindiga

Bayanan da aka samu daga wasu majiyoyi na ƴan sanda, lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 21 ga watan Yuni, da misalin ƙarfe 5:41 na yamma.

Lamarin ya auku ne lokacin da wasu mutane ɗauke da makamai, da ake zargin ƴan bindiga ne, suka kai hari kan wasu manoma da ke aikin gona a gonakinsu daban-daban.

Majiyoyin sun bayyana cewa, bayan samun rahoton gaggawa game da harin, DPO na ƙaramar hukumar ya hanzarta tura jami’an sintiri na musamman, tare da jagorantar wata tawaga mai ɗauke da mota mai sulke (APC), zuwa wurin da lamarin ya faru domin daƙile harin.

A cewar majiyar, jami’an ƴan sandan sun yi artabu mai tsanani da ƴan bindigan, inda suka tilasta musu guduwa tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Sakamakon wannan aikin ceto da rundunar ta yi, an samu nasarar kubutar da mutum shida ba tare da rauni ko lahani ba.

Wadanda aka ceto su ne, Ayuba mai shekara 51, Mubarak mai shekara 23, Garba mai shekara 25, Ibrahim mai shekara 21, Bala mai shekara 28, da kuma Nura mai shekara 25, dukkansu maza ne daga ƙauyen Tashar Nadaya.

Majiyoyin ƴan sandan sun tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ko jikkata daga cikin waɗanda aka ceto ba.

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina
'Yan sanda sun fatattaki 'yan bindiga a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

An bi sahun ƴan bindiga

Haka kuma, an bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙari wajen gano inda ƴan bindigan da suka tsere suka nufa, tare da tabbatar da cafke su domin su fuskanci hukunci.

Rundunar ta kuma yabawa haɗin kan al’umma da saurin ɗaukar mataki, inda ta buƙaci jama’a da su ci gaba da ba da bayanai masu amfani ga hukumomin tsaro domin cigaba da samun nasara a yaƙi da ta’addanci.

Abin a yaba ne

Jamilu Abubakar wanda yake zaune a jihar Katsina ya shaidawa Legit Hausa cewa nasarar da ƴan sandan suka samu abin a yaba ne.

"Wannan abin a yaba ne sosai, labarai irin waɗanan suna sanya mu cikin farin ciki. Muna addu'ar Allah ya ci gaba da taimakonsu a kan ƴan bindiga."
"Allah kuma ya kawo mana ƙarshen wannan matsalar ta rashin tsaro."

- Jamilu Abubakar

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Plateau.

Ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a wasu ƙauyuka biyu na ƙananan hukumomin Mangu da Bokkos.

Miyagun sun hallaka mutane 16 tare da ƙona gidaje masu yawa a hare-haren da suka kai cikon tsakar dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng