Labaran Duniya
Saudiya ta ce ba za ta daina kokarinta na neman 'yancin kasar Falasdinu ba, kuma ba za ta kullawata alaka ta diflomasiya da Isra'ila har sai an cimma hakan.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ba zai samu halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA 79) na wannan shekarar ba. An bayyana dalili.
A wannan labarin za ku ji yadda aka gano masu sayen kayayyaki a kasashen waje sun yi watsi da kayan abinci da aka kai masu daga Najeriya saboda algus.
Ambaliyar ruwa ta raba mutane fiye da miliyan daya da muhallansu a Maiduguri da kewaye. Majalisar Dinkin Duniya za ta kai daukin abinci da samar da matsugunni.
Masoyan fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya, Cristiano Ronaldo sun kai mutum biliyan 1. Ronaldo ya ce wannan nasarar tasa ce da masu nuna kauna a gare shi.
Asusun ba da lamuni na duniya, IMF ya ce talaka na shan wahala sosai sakamakon cire tallafin man fetur a Najeriya. IMF ya bukaci Tinubu ya saukakawa talaka.
Wani dan Najeriya daga Kano da ke aikin bincike a Korea ta Kudu, Dakta AbdulQaadir Yusuf Maigoro ya kirkiri na'urar da za ta yaki zazzabin cizon sauro.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da ziyarar aiki a kasar China. Shugaba Tinubu ya shiga wata ganawa da shugaban kasar China, Xi Jinping.
Kasar Amurka ta kwace wani jirgin shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro. Amurka ta ce gwamnatin Nicolas Maduro ta karya takunkumin da ta kakaba mata.
Labaran Duniya
Samu kari