Amurka: Wani Ɗauke da Bindiga Ya Harbe Ƴar Majalisa har Lahira, Sanata Ya Ji Rauni
- Wani mutumi ɗauke da bindiga ya shiga har gida, ya harbe ƴar majalisa tare da mijinta har lahira a jihar Minnesota ta kasar Amurka
- Rahoto ya nuna cewa bayan haka, ɗan bindigar ya farmaki sanata da matarsa, yanzu haka suna kwance a asibiti ana kula da lafiyarsu
- Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke fama da rabuwar kai a siyasa, wanda ya jawo zanga-zanga a kwanakin baya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Unuted States, USA - Wani ɗan bindiga da ba a san manufarsa ba ya harbi wasu ‘yan majalisa na jam’iyyar Democrat su biyu a jihar Minnesota ta ƙasar Amurka.
Mutumin ya kashe ƴar Majalisa ɗaya daga ciki, Melissa Hortman tare da mijinta, sannan ya raunata wani sanata da matarsa a wannan hari.

Asali: Facebook
Wannan harin ya faru ne a safiyar ranar Asabar a daidai lokacin da ake fuskantar rabuwar kawuna mafi muni a siyasar Amurka, rahoton Sky News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ƴan kwanakin da suka shige, dubban jama’a suka fara gudanar da zanga-zanga a tituna suna adawa da manufofin Shugaba Donald Trump na jam’iyyar Republican.
Jami’an tsaro sun bayyana cewa har yanzu ba a kama ɗan bindigar da ake zargi da kisan ba amma ana ci gaba da gudanar da bincike tare da farautarsa.
Shugaba Trump ya ayi Allah wadai da lamarin
Shugaba Trump da Antoni Janar na ƙasa, Pam Bondi, sun bayyana harin a matsayin “mugun abu”, inda suka sha alwashin cewa za a hukunta wanda ya aikata laifin.
A cewar Gwamna Tim Walz na jihar Minnesota, ƴar Majalisa, Melissa Hortman, tsohuwar kakakin majalisa, da mijinta Mark, sun mutu a harin da aka kai musu a gidansu da ke kusa da Minneapolis.
Gwamnan ya kara da cewa Sanata John Hoffman da matarsa Yvette su ma sun jikkata sakamakon harin, amma “akwai fatan za su samu lafiya."
Gwamna ya yi zargin harin na da alaƙa da siyasa
“Wannan hari ne na siyasa da aka yi da niyya kai tsaye,” in ji Gwamna Walz.
Shugaban Hukumar Binciken Laifuka ta Minnesota, Drew Evans, ya ce Hoffman da matarsa aka fara kai wa hari a cikin gidansu.
Ya ce bayan jami’an tsaro sun isa wajen domun kai masu ɗauki, sai mutumin ya sake kai farmaki kan ƴan Majalisar da aka kashe tare da mijinta.

Asali: Getty Images
Evans ya ce lokacin da jami’an tsaro suka yi musayar wuta da wanda ake zargi a kusa da gidan Hortman, ya samu damar tserewa.
“Yanzu haka muna ci gaba da farautar mutumin nan,” in ji shi.
Hukumomi sun bayyana cewa wanda ya kai harin yana sanye da kayan jami’an tsaro, yana amfani da hakan wajen yaudarar mutane, rahoton Channels tv.
Trump ya hana ƴan kasashe 12 shiga Amurka
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka da ta haramta wa ‘yan ƙasashe 12 shiga Amurka.
Trump ya ce an dauki matakin ne domin kare lafiyar Amurkawa daga haɗarin da ke zuwa daga wasu kasashen waje.
Bugu da kari, Shugaban Amurka ya jaddada cewa nan gaba gwamnatinsa za ta iya kara yawan waɗannan ƙasashe da za a hana shiga ƙasar.
Asali: Legit.ng