Labaran Duniya
Kamfanoni hudu daga kasashen Togo da Benin sun gaza biyan Najeriya dala miliyan 14.19 na kudin wutar lantarkin da aka tura masu a watanni 3 na farkon 2024.
Daliban da suka kifar da gwamnatin kasar Bangladesh a yayin zanga zanga sun bayyana halin da suke ciki a asibiti. Ma'aikatan lafiya ta bayyana yadda suke aiki.
An kama Yomi Jones Olayeye, dan shekara 40 dan Najeriya daga Legas, a filin jirgin sama na John F. Kennedy da ke birnin New York bisa zargin zamba na COVID-19.
Rahotanni sun bayyana cewa Maria Branyas, wadda ta fi kowa a duniya ta mutu tana da shekaru 117. An ruwaito cewa an haifi Maria a 1907 kuma ta mutu a Spain.
Wani matashi daga Arewacin Najeriya, Dakta Attahiru Dan-ali, ya yiwa dalibai bayanin abubuwan da ake bukata domin neman tallafin karatu a kasashen ketare.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da bullar cutar kyandar biri da aka fi sani da mpox a Jamhuriyar Congo da wasu kasashen Afirka. Ta yi cikakken bayani a bidiyo.
Rahotanni sun bayyana cewa fitaccen attajirin nan ɗan sharholiya, Richard Lugner ya kwanta dama bayan fama da doguwar jinya, ya rasu watanni bayan kara aure.
Matatun man fetur suna da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya. Akwai matatun mai guda 825 da ke aiki. Ga jerin guda 10 da suka fi girma.
Zinariya wata kadara ce mai kima wacce za ta iya inganta ajiyar kudin ketare, rage dogaro ga rancen kasashen waje. Mun tattaro kasashe 10 mafi samar da shi a Afrika.
Labaran Duniya
Samu kari