Kasar Musulunci Ta Iran Ta ba Amurka Hanya Mai Sauki domin Bude Mashigar Hormuz

Kasar Musulunci Ta Iran Ta ba Amurka Hanya Mai Sauki domin Bude Mashigar Hormuz

  • Babban mai shiga tattaunawar na Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce ba za a buɗe mashigar Hormuz ba har sai Amurka ta cika sharudɗa
  • Buƙatun sun haɗa da ɗage takunkuminnruwa, takunkumin mai da kuma sakin kadarorin Iran da ke ƙasashen waje
  • Ghalibaf ya ce kasar Iran a shirye take ta ƙara wa abokanta mummunar galaba idan har aka ci gaba da yaƙin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Babban mai shiga tattaunawar diflomasiyya na Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce bayyana abu daya da suke bukatar Amurka ta yi domin bude mashigar Hormuz.

Ghalibaf ya tabbatar da cewa Iran ba zata bude mashigar Hormuz mai matuƙar muhimmanci har sai Amurka ta cika buƙatun Tehran, ciki har da ɗage takunkumin ruwan da aka sanya wa Iran.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Trump ya fadi babban burin gwamnatinsa kan Iran

Hormuz.
Wasu jirage na kokarin wucewa ta mashigar ruwa ta Hormuz da ke yankin Gabas ta Tsakiya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa Ghalibaf ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 18 ga Agusta, 2026 yayin wani jawabi da aka watsa kai tsaye a gidan talabijin na ƙasar.

Abin da Iran ke bukata daga Amurka

“Ina son in bayyana a fili cewa ba za a buɗe mashigar Hormuz ba har sai an aiwatar da alkawurran da Amurka ta ɗauka a cikin yarjejeniyar fahimtar juna,” in ji Ghalibaf.

Ya bayyana daga cikin buƙatun Iran akwai ɗage takunkumin ruwa, cire takunkumin da aka kakaba wa man fetur da kuma sakin kadarorin Iran da aka rike a ƙasashen waje.

An haɗa waɗannan buƙatu cikin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka da aka cimma a watan Yunin da ya gabata, wadda daga baya ta wargaje.

Yaƙin kasar Iran da Amurka

Yaƙi tsakanin Iran da Amurka ya ɓarke a ranar 28 ga Fabrairu bayan hare-haren Amurka da Isra’ila kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da ya jawo rikici a faɗin yankin.

Kara karanta wannan

EFCC ta kai wani mutum kotu kan zargin baba kere da N56m na kudin aikin hajji

Ƙoƙarin diflomasiyya tun daga ranar 8 ga Afrilu, 2026 ya kawo ƙarshen munanan hare-haren bama-bamai, amma ana ci gaba da samun arangama lokaci zuwa lokaci, musamman a ciki da kuma kewayen mashigar Hormuz.

Iran ta ci gaba da nuna iko da mashigar tun bayan ɓarkewar yaƙin. Mashigar na da matuƙar muhimmanci ga zirga-zirgar makamashi a duniya.

Iran ta buƙaci jiragen ruwa su nemi izini tare da biyan kuɗin haraji, matakin da Washington da wasu ƙasashen yankin suka yi adawa da shi.

Mohammad Bagher Ghalibaf
Shugaban majalisar dokokin Iran kuma jagoran tawagar tattaunawa, Mohammad Bagher Ghalibaf Hoto: Handout
Source: Getty Images

Iran da Oman na tattaunawa

Iran da Oman, waɗanda dukkansu ƙasashe ne da ke gabar mashigar Hormuz, sun shafe makonni suna tattaunawa kan makomar zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar.

Tehran ta ce ƙasashen biyu sun riga sun amince da “ma’aunin yanayin ƙasa na hanyar” da aka tsara domin zirga-zirgar jiragen ruwa.

A ranar Litinin, Iran ta ce tattaunawar na “ci gaba cikin tsanaki”, yayin da ɓangarorin ke musayar ra’ayoyi kan daftarin “sanarwar haɗin gwiwa”

Burin Amurka kan kasar Iran

Kun ji cewa shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana babban burin da gwamnatinsa take da shi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Trump ya sake jaddada cewa hana Iran mallakar makamin nukiliya shi ne babban burin farko na gwamnatinsa a duk wannan rikicin da ke faruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262