'Gatan da Iran Ta Yi Wa Musulunci da Musulmi': Sheikh Ya Goyi bayan Hari kan Isra'ila

'Gatan da Iran Ta Yi Wa Musulunci da Musulmi': Sheikh Ya Goyi bayan Hari kan Isra'ila

  • Sheikh Abdallah Mahmud Adam ya bayyana goyon bayansa ga Iran duk da bambancin aƙida, yana mai cewa yanzu Musulunci ne ke gaba da komai
  • A cewarsa, Musulmi su daina kallon rikici ta fuskar kungiyanci ko mashabanci, su duba abin da zai amfani da Musulunci gabaɗaya
  • Ya ce waɗanda aka ɗora akan siyasar rudani da ƙiyayya ba za su gane manufarsa ba, domin ƙwaƙwalwarsu ta cika da hargitsi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Damaturu, Yobe - Yayin da ake cigaba da rigima tsakanin Iran da Isra'ila, malamai na fadin albarkacin bakinsu kan lamarin.

Sheikh Abdallah Mahmud Adam ya fadi matsayarsa kan rikicin da ake yi yanzu haka tsakanin kasashen biyu.

Sheikh ya magantu kan rigimar Isra'ila da Iran
Sheikh Abdallah Mahmud Adam ya fadi matsayarsa kan rigimar Isra'ila da Iran. Hoto: Sheikh Abdallah Mahmud Adam.
Asali: Facebook

Matsayar Sheikh kan fadan Iran da Isra'ila

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya goyi bayan kasar Iran duk da cewa suna da bambancin aƙida da sabani a wasu ɓangarori.

Shehin ya ce a wannan lokaci babu abin da ake magana a kai sai addinin Musulunci ba wai lamarin kungiyanci da akida ba ne.

Yayin da yake magana, Sheikh Abdallah ya ce:

"Iran mun bambanta da ita, mu da muke kan aƙidar Salafiyya, mun sha bamban da su ta fuskar aƙida.
"Amma komai kin Allah da kin gaskiyarka a duniyar da muke ciki a yanzu, sun zama gata ga Musulunci da Musulmi.
"Mu maganar Musulunci muke ba maganar akida ko mashabanci ko kungiyanci ba."
Malami ya fadi matsayarsa kan fadan Isra'ila da Iran
Sheikh Abdallah Mahmud Adam ya goyi bayan Iran. Hoto: Sheikh Abdallah Mahmud Adam.
Asali: Getty Images

Sheikh ya soki wadanda ke bayan kungiyanci

Sheikh Abdallah ya ce mafi yawan wadanda aka cusa musu shirme da hargitsi a kwakwalwarsu ba za su fahimci zancensa ba.

Ya ce wasu kwata-kwata ba su fahimtar irin wannan lamari idan bai shafi ko kuma bai yi daidai da abin da aka daura su a kai ba.

"Don maganganun nan nawa duk wanda aka cika masa kwakwalwarsa da rudanin siyasar duniya da mashabanci da kungiyanci ba zai taba fahimtarsu ba.
"Domin shi an suranta masa wani abu ne daban sabanin Musulunci saboda haka shi bangaranci shi ne abin da yake karewa.
"Daman idan ka zo kana magana kan 'Alwaki'ul Islami' shi ba wannan yake dubawa ba, an gina shi ne a kan hargitsi da shirme aka gina shi.
"Shi ganinka ya ke yi a matsayinsa wanda ba ka fahimta ba ko ba ka gane ba, yana da abin da zai jefe ka da shi."

- Cewar malamin

Tun a baya, wasu malamai suna kin goyon bayan Iran saboda bambancin aƙida da kungiyanci da ke tsakaninsu.

Iran ta kai mummunan farmaki kan Isra'ila

A baya, mun ba ku labarin cewa rahotanni sun tabbatar da cewa ƙasar Iran ta kai hari da makama kan Isra'ila a matsayin ramuwar gayya.

Wannan hari ya biyo bayan matakin Isra'ila na kai farmaki kan sojojin Iran da cibiyoyin nukiliya.

Ayatollah Khamenei ya yi alkawarin rusa Isra'ila, yayin da Donald Trump ke gargadin Iran da ta cimma yarjejeniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.