Abin Al’ajabi: Mutum 1 Ya Tsira a Hatsarin Jirgin Indiya, Ya Fadi abin da Ya Faru

Abin Al’ajabi: Mutum 1 Ya Tsira a Hatsarin Jirgin Indiya, Ya Fadi abin da Ya Faru

  • Mutum daya tilo dan asalin Burtaniya daga cikin fasinjoji 242 ya tsira a hatsarin jirgin Air India, wanda ya faru a ranar Alhamis
  • Yayin da Vishwash Kumar Ramesh, ya ce komai ya faru ne a kan idonsa, ya ce ya tsira daga hatsarin ne lokacin da ƙofar jirgin ta buɗe
  • Jirgin ya fado kan gidajen mutane a Ahmabad jim kadan bayan tashinsa, kuma Ramesh ya ce ya ji lokacin da injin jirgin ya fara ƙara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Indiya – An samu mutum daya tilo daga cikin mutane 242 da hatsarin jirgin Air India ya yi hatsari da su jim kadan bayan tashi a Ahmabad.

Vishwash Kumar Ramesh, dan asalin Burtaniya, ya ce shi kansa yana mamakin yadda ya tsira da ransa daga tarwatsewar jirgin bayan faduwarsa.

Wanda ya tsira daga hatsarin jirgin Indiya ya bayyana yadda ya tsira da ransa
Vishwash Kumar Ramesh, dan asalin Burtaniya ya tsira daga hatsarin jirgin Indiya da ya kashe fasinjoji 241. Hoto: UGC
Asali: UGC

Mutu 1 cikin 242 ya tsira a hatsarin jirgin Indiya

A yayin da yanke kwance a asibiti, yana magana da gidan talabijin na gwamnatin Indiya, watau DD News a ranar Juma'a, Vishwash ya ce "komai ya faru a kan ido na, amma ban san zan tsira ba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin Air India Boeing 787-8 Dreamliner, wanda ke cike da mai domin doguwar tafiya zuwa London, ya fado kasa tare da kamawa da wuta jim kadan bayan ya tashi daga filin jirgi a ranar Alhamis.

Vishwash Ramesh, wanda 'yan sanda suka ce yana zaune a kujera mai lamba 11A, shi ne kadai daga cikin fasinjojin da bai mutu ba, inda wasu mutum 24 da ke kusa da waje suka mutu.

"Na ɗauka cewa ni ma zan mutu" - Viswashkumar

A rahoton da gidan talabijin ya ruwaito, Ramesh Viswashkumar, yana zaune ne a kusa da ƙofar da ake fita daga jirgin idan matsala ta samu, kuma ya tsira ta hanyar ƙofar da ta bude.

An rahoto cewa an dauke shi a bidiyo bayan haɗarin jirgin a ranar Alhamis yana rangaji a kan titi, sanye da riga mai jini da raunuka a fuskarsa.

"Har yanzu ban yadda na tsira daga hatsarin ba. Na ɗauka cewa ni ma zan mutu," in ji Viswashkumar mai shekaru 40.

Ya ƙara da cewa:

"Amma da na buɗe idona, sai na gane cewa ina da rai na. Na yi ƙoƙarin cire madaurin kujerar, na kuma gudu ta kofar a ta karye. A kan ido na ma'aikatan jirgi da wasu suka mutu."
Jami'ai na ci gaba da gudanar da bincike don gano fasinjojin da suka bace ko suka mutu a hatsarin jirgin India
Yadda jirgin saman India ya fada kan gidajen mutane jim kadan bayan tashinsa a Ahmabad. Hoto: Sam PANTHAKY / AFP
Asali: Getty Images

'Yadda jirgin ya yi hatsari bayan tashi' - Viswashkumar

A ranar Juma’a, ma’aikatan ceto suka kaddamar da bincike mai zurfi don gano mutanen da suka bace da kuma sassan jirgin da suka ɓace a cikin gine-ginen da suka kone.

Viswashkumar ya ce jirgin ya tsaya a sararin sama na ɗan lokaci bayan tashi daga filin jirgi, sannan fitilun cikin jirgin masu launin kore da fari suka kawo haske.

Ya ce ya ji lokacin da injin jirgin ya fara yin ƙara sosai, sai kuma ya sullubo kasa, ya yi da gidajen mutane tare da kamawa da wuta.

Likitoci sun bayyana cewa Vishwash Kumar Ramesh bai samu wani mummunan rauni ba, lamarin da ya zamo abin al'ajabi ga kowa, inji rahoton BBC.

An samu barazanar bam a jirgin India

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani jirgin saman Air India ya yi saukar gaggawa a birnin Phuket na ƙasar Thailand jim kaɗan bayan tashinsa ranar Juma'a.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya dawo filin da ya tashi ne bayan samun saƙon barazana da ke nuna cewa an dasa bam a ɗakin wanka da ke cikin jirgin.

Kawo yanzu dai ba a ga wani bam ba a cikin jirgin ba, duk da cewa an sauke dukkanin fasinjoji tare da bincike bandakin jirgin bayan saukarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.