Zambia: Tsohon Shugaban Ƙasa, Lungu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Yana da Shekaru 68
- Tsohon shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu, ya rasu yana da shekaru 68, kamar yadda jam’iyyarsa ta sanar cikin wani jawabi
- Lungu ya jagoranci Zambia na tsawon shekara shida (2015 zuwa 2021), kafin ya fadi zabe a hannun shugaba mai ci, Hakainde Hichilema
- A wani bidiyo, ’yarsa Tasila Lungu ta bayyana cewa tsohon shugaban kasa ya yi fama da jinya a 'yan makonnin da suka gabata, kafin ya rasu a wani asibiti a kasar Afirka ta Kudu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zambia - Tsohon shugaban ƙasar Zambia, Edgar Chagwa Lungu, ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya yana da shekaru 68 a duniya.
Jam'iyyarsa ta Patriotic Front ta tabbatar da rasuwar Lungu, wanda ya shugabanci ƙasar Zambia na tsawon shekaru shida daga 2015 zuwa 2021.

Asali: Twitter
A cewar rahoton BBC, Lungu ya rasu ne da safiyar Alhamis, 5 ga Yuni, 2025, bayan samun kulawa ta musamman a wani asibiti a Pretoria da ke ƙasar Afirka ta Kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da rasuwar tsohon shugaban Zambia
‘Yarsa, Tasila Lungu-Mwansa, ta bayyana hakan a cikin wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta, rahoton Leadership.
A lokacin mulkin Shugaba Michael Sata, Lungu ya rike mukaman ministan shari’a da kuma ministan tsaro.
Bayan rasuwar Sata a watan Oktoba 2014, jam’iyyar Patriotic Front ta zaɓi Lungu a matsayin ɗan takara a taronta da aka gudanar a Kabwe.
Jam'iyyar ta tsaida Lungu a matsayin wanda zai fafata a zaben cike gurbi, inda ƴan Zambia suka zaɓi wanda ya ƙarisa wa'adin marigayi Sata.
Tarihin siyasar Marigayi Edgar Lungu
A wannan zaben, Lungu ya lallasa dan takarar adawa Hakainde Hichilema da kyar, inda ya kama aiki a matsayin shugaban kasa a ranar 25 ga Janairu, 2015.
An zabi Edgar Lungu a matsayin shugaban kasa na cikakken wa’adi a zaben watan Agusta 2016, ya sake kayar da Hakainde Hichilema da kyar.

Asali: Twitter
Hichilema ya fara kin amincewa da sakamakon zaben, inda ya shigar da kara a kotun kundin tsarin mulki domin neman soke sakamakon.
Sai dai, a ranar 5 ga Satumba, 2016, kotun ta yi watsi da karar tare da tabbatar da nasarar Lungu.
An rantsar da shi a karo na farko a matsayin shugaban kasa mai cikakken wa’adi a ranar 13 ga Satumba, 2016.
A shekara ta 2021, Lungu ya sha kaye a hannun tsohon dan adawa, Hakainde Hichilema wanda ya fafata da shi a zaben 2015 da 2016.
Fitaccen marubucin Kenya ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa shahararren marubucin nan ɗan ƙasar Kenya, Ngũgĩ wa Thiong’o, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 87 a duniya.
Marigayin ya shahara a matsayin marubuci mai tsantsar salo na adabin Afirka, tare da kirkirar litattafan yara da kuma bayyana rashin jin dadinsa kan rashin daidaito da zalunci.
A watan Maris na 2024, aka samu labarin cewa marigayin na fama da cutar ƙoda kuma yana rayuwa shi kaɗai tare da kulawar jami’an lafiya a gidansa da ke California a Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng