Duk da Gargaɗin Amurka, Iran Ta Kai Harin Ramuwar Gayya kan Isra'ila
- Rahotanni sun ce ƙasar Iran ta kai hari da makama kan Isra'ila a matsayin ramuwar gayya
- Wannan hari ya biyo bayan matakin Isra'ila na kai farmaki kan sojojin Iran da cibiyoyin nukiliya
- Ayatollah Khamenei ya yi alkawarin rusa Isra'ila, yayin da Donald Trump ke gargadin Iran da ta cimma yarjejeniya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Majiyoyi sun tabbatar da cewa Iran ta harba makamai masu linzami kan ƙasar Isra’ila.
An kai harin ne a matsayin ramuwar gayya, bayan farmakin da ya nufi manyan hafsoshin sojojin Iran da wuraren nukiliya.

Asali: Getty Images
Iran ta kai harin ramuwar gayya Isra'ila
An ji karar kararrawar barazana da fashewa a sassan Isra’ila bayan Fira Minista Benjamin Netanyahu ya ce yana sa ran jerin hare-hare daga Iran, cewar rahoton CNN.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani dan jarida ya ce hayaki na fitowa daga ginin manyan bene a Tel Aviv, yayin da Iran ta ce ta kai hari kan wurare da dama.
Hukumar kashe gobara ta ce wasu mutane sun makale a wani bene a tsakiyar Isra’ila.
Harin ya biyo bayan cewar Isra’ila ta kashe manyan janar-janar na Iran, ciki har da kusan duka shugabannin rundunar sojin sama ta Iran.
Yayin da bangarorin biyu ke kai wa juna farmaki, jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yi alkawarin rusa Isra’ila a cikin jawabin talabijin.
Khamenei ya ce:
“Dakarun Jamhuriyar Musulunci za su kai hari mai muni kan wadannan makiya.”
Buƙatar Trump kan rigimar Iran/Isra'ila
Bayan hare-haren, Donald Trump ya bukaci Iran da ta “kulla yarjejeniya” kan shirinta na nukiliya, yana gargadin hare-hare masu tsanani.
Amurka ta bayyana cewa ba ta da hannu a harin Isra’ila, amma ta gargadi Iran kada ta kai hari kan dakarunta, Aljazeera ta ruwaito.
Netanyahu ya ce Isra’ila ta kai hari kan “tushen shirye-shiryen nukiliyar Iran,” ciki har da masana da cibiyar Natanz.
Fira Ministan Isra’ila ya ce hare-haren za su ci gaba “har tsawon kwanaki da ya dace,” domin dakile shirin Iran.

Asali: Getty Images
Harin da ya kashe manyan sojojin Iran
Hare-haren sun kashe hafsan hafsoshin soja na Iran, Mohammad Bagheri, da shugaban rundunar sojin juyin juya hali, Hossein Salami.
Ministan harkokin waje Abbas Araghchi ya ce Iran ba za ta nuna hakuri da Isra’ila ba, duk da kiran da ake yi.
Khamenei ya nada sababbin kwamandoji don maye gurbin wadanda suka mutu, sai dai wani mai ba shi shawara ya jikkata.
Sojojin Isra’ila sun ce shugabannin sojojin sama na Iran sun taru a karkashin kasa domin shirya hari kan Isra’ila, kuma yawancinsu sun mutu.
Iran ta tabbatar da mutuwar kwamandan sararin samaniyar rundunar, tare da wasu jarumai masu sadaukarwa.
Hotuna sun nuna wani rami babba a wani gida a Tehran da ake zargin an kai hari a kai.
Jaridun gwamnati sun ce hare-haren da kariya daga harin iska sun ci gaba a daren Juma’a, musamman a Arewa maso Yamma.
Amurka na shirin kawo tsaiko a Gaza
Mun ba ku labarin cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an tsagaita wuta kan yaƙin da Isra'ils take yi da ƙungiyar Hamas a zirin Gaza.
Kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya ya shirya kaɗa ƙuri'a kan ƙudirin da ke neman ganin an dakatar da yaƙi a Gaza.
Sai dai, akwai yiwuwar Amurka wacce ƙawar Isra'ila ce za ta iya hana ƙudirin wucewa ta hanyar hawa kujerar na ƙi.
Asali: Legit.ng