An Ji Maganar Karshe da Matukin Jirgin Air India Ya Yi kafin Fasinjoji 241 Su Mutu

An Ji Maganar Karshe da Matukin Jirgin Air India Ya Yi kafin Fasinjoji 241 Su Mutu

  • Matuƙin jirgin Air India ya aika da saƙo na gaggawa kafin hatsarin da ya lakume rayukan mutane 241 a ranar Alhamis a Ahmedabad
  • Kyaftin Sumeet Sabharwal ya aika wa tashar jirgi cewa, "Mayday... muna rasa ƙarfin jirgin, ba zai iya tashi ba," bayan daƙiƙa 11 da tashi
  • Yayin da aka rahoto cewa jirgin ya rasa karfin tashi kuma ya fado kan gidajen mutane tare da kamawa da wuta, an ce mutum 1 ya tsira

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

India - Sabon rahoto ya nuna cewa matuƙin jirgin Air India da ya yi hatsari a Ahmedabad ya aika da saƙo na gaggawa kafin hatsarin.

A cewar rahoton sadarwar rediyo ta ƙarshe da aka bayyana wa jama'a, matuƙin jirgin ya aika da kiran gaggawa (mayday), inda ya bayyana abin da ke faruwa a cikin jirgin.

An ji maganar karshe da Kyaftin Sumeet Sabharwal ya yi kafin jirgin Air India ya yi hatsari
Kyaftin Sumeet Sabharwal, matukin jirgin Air India da ya yi hatsari a ranar Alhamis. Hoto: The Sun UK, Getty Images/amoklv.
Asali: UGC

Matukin Air India ya aika sako kafin hatsari

A cikin kalamansa na ƙarshe, matuƙin jirgin, Kyaftin Sumeet Sabharwal, ya bayyana sarai cewa jirgin Boeing 787-8 Dreamliner ya gaza samun ƙarfin tashi, inji rahoton The Sun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan yana nuna cewa jirgin bai iya samarwa kansa isasshen ƙarfin da yake bukata don tashi da kuma daidaito a sararin samaniya yadda ya dace.

Kyaftin ɗin ya kira ta hanyar na'urar sadarwarsa ta rediyo, yana mai cewa jirgin yana ci gaba da rasa ƙarfi.

A rahoton, an ji Kyaftin Sumeet Sabharwal yana cewa:

"Mayday... babu ƙarfin tashi, mun rasa ƙarfin jirgin, ba zai iya tashi sama ba."

An gaza shawo kan matsalar jirgi kafin hatsari

A cewar rahotannin da aka samu daga sadarwar rediyo tsakanin Kyaftin Sumeet Sabharwal da ma'aikatan tashar jirgin, sun nuna cewa ƙoƙarin ceto jirgin ya ci tura.

Bayan daƙiƙa 11 kacal da tashi, Kyaftin Sabharwal ya yi gargaɗin cewa "muna rasa ƙarfin jirgin."

A wannan lokacin, an ce babu wani abin da shi matukin jirgin ko sauran ma’aikatan tashar jirgin za su iya yi domin hana haɗarin da ya auku.

Air India: Yaya kwarewar Kyaftin Sabharwal take?

Captain Sabharwal yana da ƙwarewar tashi na sa’o’i 8,200, kuma yana tare da mataimakinsa Clive Kunder daga birnin Mumbai.

An ce jirgin bai yi nisa daga filin da ya tashi ba kafin faɗuwarsa. Ya faɗi a tsayin kafa 625, kamar yadda shafin Flightradar24 ya tabbatar.

Har zuwa wannan lokaci, hukumomi ba su bayana wa jama'a dalilin hatsarin da kuma dalilin da ya sa jirgin bai samu isasshen ƙarfin tashi ba.

Jirgin Air India yana ɗauke da mutane 242, kuma duk sun mutu sai mutum daya tak, wanda aka gano sunansa Vishwash Kumar Ramesh.

Matukin jirgin Air India ya aika sakon gaggawa 'yan dakiku kafin ya yi hatsari a Ahmedbad
Clive Kunder, wanda ya fito daga Mumbai, ya kasance mataimakin matuƙin jirgin Air India ada ya yi hatsari. Hoto: The Sun UK, Reuters
Asali: UGC

Jirgin Air India ya nufi London-Gatwick

Rahoto ya ce jirgin yana kan hanyarsa ta zuwa Burtaniya, inda ake sa ran zai sauka a filin jirgin sama na London Gatwick, sai dai, kaiwar da bai yi ba kenan.

An ce ya faɗa cikin wani gida da likitoci ke kwana a ciki, inda rahoton Hindustan Times ya nuna cewa wata mata ta ce ɗanta ya yi tsalle daga hawa na biyu na ginin don neman tsira.

Matar ta shaida wa manema labarai cewa:

"Ɗana yana nan lafiya, kuma na yi magana da shi. Ya yi tsalle daga bene na biyu na ginin, don haka ya samu ƴan raunuka."

Mutum 1 ya tsira daga hatsarin Air India

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani ɗan asalin Birtaniya ne kaɗai ya tsira daga cikin fasinjoji 242 da ke cikin jirgin Air India da ya yi hatsari a ranar Alhamis.

Vishwash Kumar Ramesh ya bayyana cewa komai ya faru a kan idonsa, kuma ya tsira ne bayan ƙofar jirgin ta buɗe yayin hatsarin.

Jirgin ya faɗo kan gidajen mutane a Ahmedabad jim kaɗan bayan tashinsa, inda Ramesh ya shaida cewa ya ji lokacin da injin jirgin ya fara yin ƙara mai ƙarfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.