Pakistan za Ta Taya Iran Fada, za Ta Harba Nukiliya Isra'ila

Pakistan za Ta Taya Iran Fada, za Ta Harba Nukiliya Isra'ila

  • Iran ta bayyana cewa Pakistan ta yi alkawarin kai wa Isra’ila hari da bam ɗin nukiliya idan Benjamin Netanyahu ya fara amfani da makamashin
  • Babban kwamandan IRGC a Iran, Mohsen Rezaei ya ce Pakistan ta ba su tabbacin martani mai ƙarfi idan Isra’ila ta kai mata harin nukiliya
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Pakistan ta ce makaman nukiliyarta ba don mamaya ba ne, sai dai kare kai daga abokan gaba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Ƙasashen Iran da Isra’ila sun shiga rikicin soja da ya yi tsanani, inda kowacce ke jefawa 'yar uwarta makamai masu linzami.

Biyo bayan wannan rikici, Iran ta fito fili ta bayyana wata sanarwa mai tayar da hankali cewa Pakistan ta yi alkawarin kare ta daga harin nukiliya idan Isra’ila ta fara amfani da shi.

Iran ta samu goyon bayan Pakistan
Pakistan ta bukaci a takawa Isra'ila birki. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

India Today ta wallafa cewa ɗaya daga cikin manyan jami’an tsaron Iran kuma mamba a Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iran ta tabbatar da goyon bayan Pakistan

Babban jami'in tsaro a kasar Iran, Mohsen Rezae ya tabbatar da cewa sun samu tabbacin goyon bayan Pakistan.

A cewar Rezaei:

“Pakistan ta ba mu tabbaci cewa idan Isra’ila ta fara amfani da bam ɗin nukiliya kan Iran, to su ma za su kai wa Isra’ila hari da irin makamashin.”

Sai dai wannan furuci ya janyo ce-ce-ku-ce a duniya, inda aka fara tsoron cewa lamarin na iya jawo yaki na makaman nukiliya a Gabas ta Tsakiya.

Ministan Tsaron Pakistan, Khawaja Muhammad Asif, ya wallafa a X cewa:

“Makaman nukiliyarmu domin kare kai ne da ci gaban al’ummarmu. Ba mu da wata manufa ta mamaya ko nuna karfi ga maƙwabta, sabanin yadda Isra’ila ke nunawa.”

Yaki tsakanin Iran da Isra’ila na ci gaba

A ranar Asabar Isra’ila ta kai mummunan harin sama kan wuraren soja da makaman nukiliya na Iran, wanda hakan ya janyo Iran ta mayar da martani da jefa makamai masu linzami.

Rahotanni daga Tel Aviv da Urushalima sun nuna yadda fashe-fashe suka cika sararin sama, yayin da Isra’ila ta ce ta lalata fiye da kashi ɗaya bisa uku na sansanonin harba makaman Iran.

Kaza lika, wani jigo a gwamnatin Isra’ila ya ce babu wani abu da zai hana su kai hari ko kashe jagoran Iran, Ayatollah Khamenei, matakin da ke ƙara tayar da hankali a duniya.

Pakistan ta kira kasashen Musulmi su hadu

Ministan tsaron Pakistan ya kuma gargadi ƙasashen Musulmi masu hulɗa da Isra’ila da su dakatar da alaka.

Pakistan ta bukaci Musulmai su hada kai a duniya
Pakistan ta bukaci Musulmai su hada kai a duniya. Hoto: Inside the Haramain
Asali: UGC

Ya bukaci Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (OIC) da ta kira zaman gaggawa domin tsara matakin hadin gwiwa da za a ɗauka.

Ya ce:

“Isra’ila ta kai hari kan Iran, Yemen da Falasdinu. Idan ƙasashen Musulmi ba su haɗu ba yanzu, to kowa zai fuskanci irin wannan hali.”

Iran ta kashe mutane a Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa a Iran ta kashe mutane da dama a daren Litinin bayan harba makamai masu linzami kasar Isra'ila.

Hakan na zuwa ne bayan kazamin fada ya kaure a tsakanin kasashen biyu kan mallakar makamin nukiliya.

Legit ta rahoto cewa Iran ta ce ba za ta yarda da shirin tsagaita wuta ba matukar Isra'ila na cigaba da kai mata hare hare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng