Dalilin da Ya sa Musulunci Ya Zamo Addini Mafi Habaka a Fadin Duniya
- Wani sabon bincike ya nuna cewa Musulunci ne addinin da ya fi karuwa a duniya tsakanin shekarar 2010 zuwa 2020
- Rahoton ya ce karuwar ba ta da alaka da sauya addini, sai dai yawan haihuwa da kuma karin matasa da yawa a cikin Musulmai
- Yayin da Kiristanci ke raguwa a kasashe da dama, adadin Musulmai ya karu musamman a kasashen da suka fi yawan Musulmai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sabon rahoto daga cibiyar bincike ta Pew ya bayyana cewa addinin Musulunci ne ya fi karuwa a duniya cikin shekaru goma da suka gabata, wato daga 2010 zuwa 2020.
Binciken da aka fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa yawan haihuwa a tsakanin Musulmai ne suka haifar da karuwar, ba wai sauya addini ba.

Asali: Twitter
A cewar rahoton Middle East Eye, yawan Musulmai ya karu fiye da duk wasu addinai, inda hakan ya sanya Musulunci zama addinin da ke karuwa da sauri a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin karuwar Musulmi a fadin duniya
Rahoton NPR ya nuna cewa cibiyar Pew ta bayyana cewa Musulmai na haihuwar yara da dama yayin da wadanda da ba Musulma ba ke haihuwar yara kadan.
Rahoton ya bayyana cewa:
“Musulmai suna da yara da yawa kuma su kan fi sauran addinai yawa."
Wannan yana nuna cewa yawan Musulmai ya fi karuwa ne ta hanyar haihuwa da samun ‘ya’ya, maimakon mutane masu sauya addini zuwa Musulunci.
Musulunci na cike gibin da ke tsakaninsa da Kiristanci
Duk da cewa Kiristanci har yanzu shi ne addini mafi yawan mabiya a duniya da kusan mutane biliyan 2.3, binciken ya nuna cewa tazara tsakanin Musulunci da Kiristanci na raguwa.
Rahoton ya bayyana cewa Kiristanci ya ragu da kashi 1.8 tun daga shekarar 2010, inda aka samu sauye-sauyen mabiya zuwa wasu addinai ko kuma barin addini kwata-kwata.
A kasashe 40, adadin Kiristoci ya ragu da akalla kashi 5, yayin da aka samu karin Kiristoci sosai a kasashe guda kawai.
Musulunci ne kadai samun karin mabiya ba ragi
Daya daga cikin manyan abubuwan da rahoton ya gano shi ne cewa Musulunci ne kadai addinin da ya samu karin mabiya ba tare da raguwa ba.
Rahoton ya ce:
“Addinan Budda da Hindu suma sun fuskanci matsalar barin addini daga mutane fiye da yawan wadanda suka shigo cikinsu,”
A daya bangaren kuma, Musulunci ya samu karin mutane da suka shigo addinin fiye da wadanda suka fita.

Asali: Facebook
Yawan wadanda ba su da addini na karuwa a Turai
Rahoton ya kuma gano cewa yawan wadanda ba su da wani addini ya karu sosai a kasashen yamma, musamman Amurka inda aka samu karin kashi 97 na wadanda ba sa bin wani addini.
A kasar China kuwa, mafi yawan wadanda ba su da alaka da addini suna zaune kawai na karuwa, inda adadin su ke ninkuwa a kullum.
Rahoton Pew ya sanya Musulunci a matsayin addini mafi karfi a duniya, kuma ana sa ran wannan cigaba zai ci gaba a shekaru masu zuwa.
Limamin Arafa ya yi kira ga Musulman duniya
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Sale Ibn Abdallah Al Humaid ya ja hankalin Musulman duniya a hudubar Arafa ta 2025.
Malamin ya bukaci al'ummar Musulmi da suka samu damar zuwa aikin Hajji a bana da su saka sauran 'yan uwansu a addu'a.
Baya ga haka, malamin ya fadi hanyoyin da kowane musulmi zai bi domin samun tsira a duniya da lahira yayin hudubar.
Asali: Legit.ng