Jihar Gombe
Tsohon ministan Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya sanar da rasuwar yayan mahaifiyarsa, Malam Abubakar Audu wanda ya rasu yana da shekaru 110 a duniya.
Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya sanar da kammala gyaran wuta a yankin Arewa maso gabashin Najeriya. A yau Talata kamfanin ya sanar da kammala aikin.
Gwamnatin Gombe za ta kashe naira biliyan 20 kan gina titi mai tsawon kilomita 18.5 a ciki da wajen kwaryar jihar. Kwamishinan ayyuka na jihar ne ya sanar da haka.
Hukumar EFCC reshen jihar Gombe ta kama wani matashi da ya yi bidiyo yana manna kudi a gidan rawa. Matashin mai suna Zachariyya Muhammad ya amsa laifinsa.
Ministan sufuri, Sanata Sai'du Ahmed Alkali ya kaddamar da tashar zamani mai suna Tashar Ibrahim Hassan Dankwambo a Gombe. Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranci bikin.
Sheikh Isa Ali Pantami ya tabbatar da karbar mutumin da ya fara tattaki domin zuwa wajensa a Abuja. Ya kuma bayyana cewa idan ya huta za a maido shi Gombe.
Babban malamin addinin Musulunci sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya dakatar da wani matashi mai suna Auwal da yake kokarin tattaki zuwa wajensa a Abuja.
Jami'an hukumar EFCC sun kama Janty Emmanuel bisa zargin cin zarafin kudin Najeriya a Gombe. Matashiyar ta amsa laifinta bayan an nuna mata bidiyo.
Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya aike da sakon ta'aziyya yayin da aka rasa daya daga cikin dattawan jihar Gombe, Gidado Bello Akko a jiya Lahadi a Zariya.
Jihar Gombe
Samu kari