Akwai Matsala: Amurka Ta Aika Sako Mai Zafi, Ta Kafa Sharadin Komawa Yaki da Iran
- Gwamnatin Amurka ta yi barazanar komawa fagen yaki da kasar Iran matukar tattaunawar sulhun da aka fara ta gaza cimma nasara
- Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai da ya gudanar a birnin Washington DC
- Wannan gargadi na zuwa ne yayin da Amurka ta kafa dokar hana duk wata zirga-zirgar jiragen ruwa a tashohin Iran domin matsa wa kasar lamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Dakarun sojojin Amurka sun shirya tsaf domin ci gaba da yakar kasar Musulunci ta Iran idan tattaunawar sulhu ba ta yi nasara ba.
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ne ya bayyana hakan, inda ya ce ƙasar ashirye take ga sake komawa fagen daga idan Iran ta ƙi amincewa da yarjejeniya a tattaunawar da ake yi tsakanin ɓangarorin biyu.

Kara karanta wannan
Ana shirin sake zama, Trump ya fadi abin da zai harzuka Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Source: Getty Images
Amurka ta sake gargadin kasar Iran
Hegseth ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Alhamis yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin Washington DC, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta ruwaito.
Ya ce rundunar sojin Amurka tana cikin shirin ko-ta-kwana domin fara kai sababbin hare-hare idan hanyoyin diflomasiyya suka kasa haifar da sakamako mai kyau.
Ya kuma yi iƙirarin cewa rundunar ruwan Amurka na kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, yana mai cewa Iran “ba ta da rundunar ruwa a yanzu."
Ministan ya ƙara da cewa Amurka za ta ci gaba da killace tashohin ruwa na Iran na tsawon lokacin da ya dace, yana nuna cewa babu wani shiri na sassauta wannan mataki a kan Tehran nan kusa.
Ministan Amurka ya aika sako ga Iran
A cikin wani sako mai ƙarfi ga shugabannin Iran, Hegseth ya bayyana cewa Amurka na sa ido sosai kan duk wani motsin sojin Iran da kayayyakin yakinta.

Kara karanta wannan
Ana kokarin sulhu, Amurka ta gano halin da jagoran Iran, Khamenei ke ciki bayan kai masa hari
“Muna kallon ku,” in ji shi, yana nufin dukkan ayyukan da Iran ke yi a fannin tsaro da soja, kamar yadda jaridar Indian Today ta kawo.
Ya kuma gabatar da zaɓi mai muhimmanci ga Iran, inda ya ce ƙasar za ta iya zaɓar hanya mai kyau ta ci gaba da walwala da zaman lafiya, ko kuma ta fuskanci sakamako mara dadi idan ta ƙi amincewa da tattaunawa.

Source: Facebook
Wannan sabon gargaɗi ya zo ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Washington da Tehran ke ƙara ƙamari, duk da cewa ana ci gaba da tattaunawa ta bayan fage domin samun mafita mai dorewa.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya suna cikin shirin ko ta kwana, yayin da gwamnatin Amurka ke bin hanyoyin diflomasiyya da kuma matakan soja domin matsa wa Iran lamba.
Amurka ta samu alheri a yakin Iran
A wani labarin, kun ji cewa yaki da kasar Musulunci ta Iran ya zama alheri ga kasar Amurka wajen fitar da danyen mai zuwa kasashe daban-daban a duniya.
Amurka na dab da zama mai fitar da danyen mai fiye da yadda take shigowa da shi cikin kasar a makon da ya gabata, karon farko tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu.
Hakan ta faru ne sakamakon ƙaruwar buƙatar mai daga kasashen Turai da Asiya, wanda ya samo asali daga yakin da ya auku a Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng