Mutanen Gombe sun kai ƙarar Pantami Kotu kan neman takarar gwamna a zaɓen 2023

Mutanen Gombe sun kai ƙarar Pantami Kotu kan neman takarar gwamna a zaɓen 2023

  • Wasu tawagar mutane a jihar Gombe sun maka Ministan Sadarwa, Isa Pantami a gaban Kotu kan kujerar gwamna
  • Shugaban ƙungiyar mutanen ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ne domin tilasta masa ya nemi takarar gwamna a Gombe
  • A cewarsu, Nasarorin da jagoran ya samu kaɗai sun isa su jawo hankalin mutane su yi kwaɗayin ya shugabance su

Gombe - Wasu mazaunan jihar Gombe masu kishi sun shigar da ƙara gaban babbar Kotu kan Minista harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Pantami, domin tilasta masa ya tsaya takarar gwamna a 2023.

Mutanen daga gundumomi 114 dake faɗin jihar Gombe sun shigar ƙarar ne ranar 21 ga watan Maris, 2022, kamar yadda Jaridar Punch ta rahoto.

Shari'ar wacce aka shigar da Pantami da kuma jam'iyyar APC mai mulki zata gudana ne ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a A.Y Abubakar na babbar Kotun jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Tinubu @ 70: Buhari ya tura masa sakon taya murna, ya fadi halayen Tinubu na kirki

Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami.
Mutanen Gombe sun kai ƙarar Pantami Kotu kan neman takarar gwamna a zaɓen 2023 Hoto: Farfesa Isa Pantami/Facebook
Asali: Facebook

Da yake jawabi a wurin taron manema labarai, shugaban tawagar mutanen da suka shigar da ƙarar, Muhammad Abdullahi, ya ce tsohon shugaban NITDA ya nuna kyakkyawan jagoranci da taimakom matasa a Gombe da ƙasa baki ɗaya.

A cewar Abdullahi, duk wani yunkuri na jawo hankalin ministan ya fito takarar gwamna ya gagara, inda ya ƙara da cewa sun yi amanna cewa Ministan ne ya fi da cewa ya karbi jihar.

Ya ce:

"Domin tabbatar da abin da muke nufi dagaske ne yasa zami amfani da doka wajen tilasta wa Farfesa Isa Pantami ya fito takara a fafata da shi a zaɓen fidda gwani na kowace jam'iyga yake so."
"Mutane 114 daga yankuna 114 da muke da su a Gombe, mun yanke siya masa Fam ɗin takara. Muna fatan wannan ƙara ta fargar da jagoran mu, Pantami."

Kara karanta wannan

Yan takarar shugaban ƙasa uku na PDP sun haɗa sabuwar tafiya, sun shirya kwace mulki a 2023

Kazalika ya bayyana cewa nasarorin da Pantami ya samu a tarihi yasa suka ɗauki wannan matakin domin jawo hankalinsa.

A wani labarin na daban kuma An fara gano yawan mutanen da suka mutu a harin jirgin ƙasan Kaduna

Wata majiya a kusa da tsahar jirgin ƙasa dake Rigasa Kaduna ta ce ana tsammanin fasinjoji Bakwai suka mutu a harin.

Tuni dai hukumar sufurin jiragen ƙasa ta kasa ta dakatar da jigila a hanyar biyo bayan harin da yan ta'adda suka kai wa jirgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel