Babban jigon jam'iyyar PDP a jihar Gombe ya sauya sheka zuwa APC mai mulki

Babban jigon jam'iyyar PDP a jihar Gombe ya sauya sheka zuwa APC mai mulki

  • Tsohon hadimin tsohon gwamnan jihar Gombe, Barista Abdulƙadir Yahaya, ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar APC mai mulki
  • Tsohon mashawarci kan harkokin siyasa ya ce ya ɗauki wannan matakin ne saboda ɗumbin ayyukan cigaba da gwamna ke yi
  • Ya tabbatar da cewa a shirye yake ya taimaka wajen ganin gwamna Inuwa Yahaya ya zarce kan mulki a 2023

Gombe - Jigon jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Barista Babagoro Abdulƙadir Yahaya, ya tabbatar da sauya sheƙa daga jam'iyyar zuwa APC, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Barista Yahaya, wanda tsohon mashawarci kan harkokin siyasa ne ga tsohon gwamna, Ibrahim Dankwambo, ya bayyana haka ne a wurin taron manema labarai ranar Lahadi.

Jam'iyyar PDP ta kara samun cikas a Gombe.
Babban jigon jam'iyyar PDP a jihar Gombe ya sauya sheka zuwa APC mai mulki Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Yace ya ɗauki matakin komawa jam'iyya mai mulki ne saboda ɗumbin ayyukan cigaba da gwamna Inuwa Yahaya ke aiwatarwa al'ummar Gombe.

Kara karanta wannan

Gwamnan Adamawa ya faɗi sunan wanda PDP zata tsayar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023

Ya kuma yaba wa gwamnati mai ci kan ayyukan hanyoyi daban-daban da ta gudanar da kuma ɗumbin ayyukan samar da ruwan sha da ta kafa tushen farawa a faɗin jihar.

Ina goyon bayan tazarce - Barista Yahaya

Tsohon mashawarci kan harkokin siyasa, wanda ya ayyana cewa ba abinda PDP zata iya yi yanzu, ya ce a shirye yake ya ba da gudummuwa wajen cika kudirin tazarcen gwamnan domin ya ɗora kan wa'adi na farko.

A jawabinsa ya ce:

"Na dawo jam'iyyar APC ne domin taimaka wa gwamna a kokarinsa na canza fasalin Gombe da maida ta hanya mai kyau har wasu su fara kishi."
"Idan baku manta ba Alhaji Inuwa Yahaya ya samu nasarar lashe zaɓen gwamna duk da ba mulki a hannunsa, saboda haka, ina ganin ba abin da zai hana shi zarce wa duba da ɗumbin goyon bayan da yake da shi."

Kara karanta wannan

Dankwambo ya dawo Gombe bayan shekaru 3, ya ce har yanzu PDP ce burin talaka

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta samu gagarumin koma baya, Ɗan takarar gwamna ya yi murabus

Ɗan takarar gwamna a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP a jihar Osun ya yi murabus daga kasancewarsa mamba.

Dakta Akin Ogunbiyi, jigo a PDP reshen Osun ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyya na ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel