Wasu masu laifi sun tsere daga Ofishin yan sanda a Gombe

Wasu masu laifi sun tsere daga Ofishin yan sanda a Gombe

  • Wasu masu laifi da ake zargi sun tsere daga Ofishin yan sanda dake yankin Awak a jihar Gombe
  • An samu nasarar sake chafke uku daga cikinsu amma ana cigaba da neman sauran biyun
  • Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun hukumar yan sanda ya sanyawa hannu

Akalla masu laifi biyar ne suka tsere daga ofishin yan sanda dake yankin Awak dake karamar hukumar Kaltango a jihar Gombe.

Uku daga cikin wanda ake zargin an kama su, amma sauran biyu ana neman su har yanzu a lokacin hada wannan rahoton, kamar yadda The punch ta ruwaito.

Wannan na kunshe cikin wani jawabin manema labarai wanda mai magana da yawun hukumar yan sanda, Mahdi Abubakar ya sanyawa hannu.

Wasu masu laifi sun tsere daga Ofishin yan sanda a Gombe
Wasu masu laifi sun tsere daga Ofishin yan sanda a Gombe
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

Jawabin yace, "An jawo hankalinmu akan wani al'amari da ya faru a Kamo, Tungo Awak, na karamar hukumar Kaltungo, yayinda wasu wanda ake zargi da balla shago da sata wadanda aka damke amma daga bisani suka tsere daga hannun hukuma.

"Abinda ya faru shine mutanen kauyen Kamo- Tungo sun kama wasu mutane biyar wadanda aka ambata da Bello Ibrahim shekaru 19, Manasa Isaac shekaru 18 , Sani Bello mai shekaru 18, tare da Muhammed Yahaya, and Bello Babawuro, wadanda suka mika su hedkwatar yan sanda dake yankin Awak jihar Gombe domin daukan mataki.

Rashin kula na Jami'an yan sandan dake aiki a lokacin ne ya jawo suka tsere

"Amma saboda tsabar rashin kula na Jami'an yan sandan dake aiki a lokacin, wadanda ake zargin sun tsere daga ofishin a ranar 27/03/2022 da misalin karfe 8:30. A lokacin ne CP din yan sanda yasa jami'an tsaro suka bazama neman su kuma akayi sa'ar sake kama uku daga cikinsu, amma sauran biyun ana neman su har yanzu.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Jami'in Kwastam, Ɗansa Da Wasu Mutum 8 a Sabuwar Harin Da Suka Kai a Kaduna

Babaita ya bayyana cewa an sake chafke uku cikin masu laifin, sannan yayi kira ga mutane su ba jami'an tsaro goyan baya.

Sai an dau kwakkwaran mataki akan yan sandan

"Kwamishinan yan sandan yayi kira da a dau kwakkwaran mataki akan jami'an dasu kayi sake da aikinsu har masu laifin suka samu sauka tsere. ya kuma kara dacewa an tanadi duka abinda ake bukata na yan sanda da matakai na ganin cewa an damke sauran masu laifin da suka tsere.

"Kwamishinan ya ba mutanen kauyen Kamo- Tungo dama jihar Gombe baki daya tabbacin cewa zasu yi duk mai yiyuwa na ganin sun tsare su kuma za'a bincika tara da kama duk wani nau'in ta'addanci sannan a mika su zuwa ga kotu domin adalci. "jawabin ya kara.

A wani labarin kuma, A ranar Laraba Isah Hassan, wanda ake zargin ya tafka aika-aika, ya bayyana yadda ya kwakule wa wani Almajiri, Mustapha Yunusa, idanu duk don ya yi layar bata daga ‘yan bindigan daji yayin da ya ke zuwa yin ice a Jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye da bayanan mutanen da suka mutu a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Hassan, wanda dan asalin karamar hukumar Tarauni ne da ke Jihar Kano ya ce ya yaudari Almajirin zuwa wani wuri daga nan da karfi ya kwakule masa idanu da wuka, Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel