Abokin takararsu Atiku a zaben 2019, Dankwambo zai sake jarraba sa'ar zama Sanata a 2023

Abokin takararsu Atiku a zaben 2019, Dankwambo zai sake jarraba sa'ar zama Sanata a 2023

  • Ibrahim Hassan Dankwambo ya zama ‘dan takarar Sanatan Arewacin jihar Gombe a jam’iyyar PDP
  • Tsohon gwamnan na jihar Gombe ya samu tikiti ne bayan duk sauran ‘yan takarar sun janye masa
  • Abubakar Aliyu da Anthony Siyako Yaro za su rikewa PDP tuta a sauran mazabun jihar Gombe a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gombe - A ranar Litinin, 23 ga watan Mayu 2022, tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ya samu nasara a zaben tsaida gwani.

Daily Trust ta ce Ibrahim Hassan Dankwambo shi ne wanda jam’iyyar PDP ta ba takarar Sanata na yankin Arewacin jihar Gombe a zabe mai zuwa.

Tsohon gwamnan ya yi galaba ne a kan Sanata Usman Bayero Nafada da Abdulkadir Hamma Saleh, wanda suka hakura, suka janye masa takarar.

Usman Bayero Nafada da Abdulkadir Hamma Saleh sun aiko da takardar janye takara ta hannun wakilansu, don haka aka tsaida Ibrahim Dankwambo.

Kara karanta wannan

2023: Shahararren Mawakin Najeriya ya yi nasarar samun takarar ‘Dan Majalisa a PDP

Dankwambo shi ne ya tsayawa jam’iyyar hamayyar ta PDP takarar kujerar Sanata a Arewacin jihar Gombe, amma ya sha kashi a hannun APC a 2019.

Idan za a tuna, Sanata mai-ci, Saidu Ahmed Alkali shi ne wanda ya doke tsohon gwamnan jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shi kuma Sanata Usman Bayero Nafada ya taba rike kujerar majalisar wakilai da ta majalisar dattawa tsakanin 2007 da 2015 a ANPP, PDP da ma APC.

Ibrahim Hassan Dankwambo
Ibrahim Hassan Dankwambo Hoto: HEDankwambo
Asali: Twitter

Aliyu da Yaro sun samu tikiti

Rahoton da muka samu daga The Guardian ya bayyana cewa Alhaji Abubakar Aliyu shi ne ya samu tikitin Sanatan Gombe ta tsakiya a jam’iyyar PDP.

Alhaji Abubakar Aliyu wanda ya taba neman gwamnan jihar a jam’iyyar CPC ya samu kuri’u 59, ya doke Muhammadu Aliyu Baba wanda ya ci kuri’u uku.

Aliyu zai yi takara da duk wanda ya samu tikitin APC tsakanin Sanata Muhammad Danjuma Goje, Sanata Idris Abdullahi Umar ko Abubakar Habu Muazu.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan kwamiti sun haramtawa tsohon Sanatan PDP shiga zaben neman Gwamna a APC

Rahoton ya ce kudancin Gombe, Anthony Siyako Yaro ne ya sha da kyar bayan ya samu kuri’a 59. Yaro ya doke Hajiya Fatima Binta Bello da ta samu kuri’u 57.

Hon. Binta Bello tayi wa PDP takara a zaben da ya wuce, amma Bulus K. Amos ya yi nasara APC.

Sadiq Ango Abdullahi ya samu tuta

Rahotanni sun nuna cewa Sadiq Ango Abdullahi ya lashe tikiti a PDP, ya samu galaba a kan ‘yan takarar majalisar wakilan tarayya a Sabon Gari a Kaduna.

Sadiq Ango Abdullahi ya dade yana neman takarar ‘dan majalisa a jam’iyyar APC bai samu ba, sai a zabe mai zuwa 2023 ne ake sa ran zai jarraba sa'a a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel