Wata kungiya ga gwamnatin Gombe: Ku daina jefa yara cikin hadari da sunan siyasa

Wata kungiya ga gwamnatin Gombe: Ku daina jefa yara cikin hadari da sunan siyasa

  • Wata kungiya mai zaman kanta ta damu da yadda 'yan siyasa ke amfani da yara wajen harkokin siyasarsu
  • Kungiyar ta nema gwamnatin jihar Gombe da ta daina tara yara a makaranta da sunan tarbar gwamna yayin da ya kai ziyara
  • Wani mahaifi da malamin makaranta sun zanta da Legit.ng Hausa kan wannan yanayi da ka iya zama mai hadari ga yara

Gombe - Jaridar Punch ta ruwaito wata kungiya mai zamanta ta Association of Non Governmental Organisations (ANGO) na kira ga gwamnatin Gombe da ta daina tsunduma yara dalibai cikin harkokin siyasa ta hanyar jera su da sunan tarbar gwamna.

Wannan kira na zuwa ne biyo bayan rasuwar Rahab Hassan a ziyarar da Gwamna Inuwa Yahaya ya kai Kuma domin rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta jami’ar jihar da wata jami'ar waje mai zaman kanta a makon jiya.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Kebbi: Ku ragargaji 'yan bindiga kafin su kai hari, Buhari ga jami'an tsaro

Kungiya ta gargadi gwamnatin Gombe
Wata kungiya ga gwamnatin Gombe: Ku daina jawo mutuwar yara a yawon siyasarku | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

A cewar sanarwar da shugaban kungiyar mai zaman kanta, Ibrahim Yusuf ya fitar, ya ce kamata ya yi gwamnati ta dakatar da kawo yara 'yan makaranta cikin lamurransu, inda tace hakan ka iya jefa kananan yara cikin hadari.

A cewar wani yankin sanarwar:

“Mun lura cewa ayyukan ‘yan siyasa da magoya bayan jam’iyya mai mulki a jihar na ci gaba da sanya yanayin wasu makarantu cikin hadari da kuma barazana ga rayuwa a jihar.

Kungiyar ta bayyana cewa, jera dalibai domin tarbar 'yan siyasa ba daidai bane kuma hakan ka iya jefa rayuwar yara cikin hadari a lokutan da aka samu rikicin siyasa.

Hakazalika, kungiyar ta bayyana cewa, wannan aiki na iya jefa rayukan daliban Firamare sama da 2,500, dalibai 2,000 na kananan sakandare da 1,500 manyan sakandare na jihar cikin hadari.

Kara karanta wannan

Buhari bai lamunce mun don darewa kujerar shugaban APC na kasa ba – Sanata Abdullahi Adamu

Martanin malamin makaranta da mahaifin wasu dalibai

Legit.ng Hausa ta tattauna da jami'in kula da jarrabawa na makarantar sakandaren kimiyya ta JIBWIS da ke Gombe, Malam Sa'idu Idris Malwa kan dalilin da yasa makarantu ke jera dalibai yayin tarbar bakin 'yan siyasa.

Ya shaida mana cewa:

"Gaskiyar abin shi ne, kasan akan yi irin wannan ne domin a nunawa gwamna ko wani dan siyasa girmamawa, don haka ake kawo dalibai domin su tsaya su rera wakar yabo garesu.
"Yayin da ya kamata a ce makaranta wuri ne da bai kamata a siyasantar ba, musamman tunda akwai yara, amma dai kawai mun ga ana hakan ne, inaga shi yasa wasu ma suke kwaikwaya amma dai ina ganin ba daidai bane gaskiya."

A bangare guda, mun tuntubi wani uba mai yara shida a makarantar firamaren gwamnati ta Pantami, Haruna Musa Abdullahi kan ya zai ji idan yaransa suka tsinci halinsu a irin wannan yanayi na tsayawa domin tarbar gwamna.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bayelsa ya yabi Buhari, ya ce Shugaban kasa ya ba ‘Yan Najeriya ‘kyauta’

Ya bayyana cewa:

"Eh to, ya danganta da waye shugaban. Akwai shugabanni marasa adalci da ke tafiya da 'yan kalare. Idan irin wannan ne gaskiya ba zan ji dadi ba, kuma ma ai yanayi ne ke sa mu tura 'ya'yanmu makarantun gwamnati, idan ina da kudi zan kai 'ya'ya na makarantar kudi domin su samu kulawa mai kyau, saboda nasan ba za a yi haka a makarantun kudi ba."

Gwamna a Arewa ya ce an gano danyen man fetur fiye da ganga biliyan 6 a jiharsa

A wani labarin, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce Kamfanin Man Fetur na NNPC ta hannun wata kamfani mai neman man fetur ya gano danyen man fetur fiye da ganga biliyan 6 a yankin Kolmani.

Ya bada tabbacin cewa gwamntinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin ganin an fara hako man danyen man da aka gano a masarautar Pindiga ta Jihar Gombe, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dakatar da jirgin kai tsaye zuwa Saudiyya na iya hana 'yan Najeriya Umrah a Azumi, CSO

Inuwa ya bayyana hakan ne yayin wata liyafa da aka shirya domin karrama alkalin alkalai na wucin gadi na jihar Gombe, Hon Justice Muazu Abdulkadir Pindiga da aka yi a Pindiga a karamar hukumar Akko a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel