Mata sana'a ta fi bani: Yadda mata ta gina gidaje da sana'ar toya 'Masa' a Gombe

Mata sana'a ta fi bani: Yadda mata ta gina gidaje da sana'ar toya 'Masa' a Gombe

  • Wata mata mai sana'ar sayar da masa a jihar Gombe ta bayyana sirrin da ke tattare da sana'ar, da yadda ta fara
  • Ta shaidawa majiya cewa, ta samu damar sauya rayuwarta da 'ya'yanta ta dalilin wannan sana'a da ta rike hannu bibbiyu
  • Ya kuma bayyana kiraye-kiraye ga jama'a da su riki kananan sana'o'i domin rike kai ba wai jiran ayyuka masu tsoka ba

Misis Rebecca Dung, mai sayar da fitaccen kayan ciye-ciye a Arewacin Najeriya “masa” ta shawarci matasa da mata da su rika shiga kananan sana’o’i domin su iya rike kansu.

Dung, wacce ta ba da wannan shawarar a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Gombe, ta ce ta gina gidaje biyu daga kudaden da take tarawa a sana'ar sayar da kayan abinci a kusa da otal din Jiyamere da ke Gombe.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Sana'a ta haifar wa mata mai 'ya'ya.3 da mai ido
Mata sana'a ta fi bani: Yadda mata ta gina gidaje da sana'ar toya 'Masa' a Gombe | Hoto: NAN News, @GoronBauchi
Asali: UGC

Matar mai ‘ya’ya uku ta bayyana cewa ta fara sana’ar masa ne shekaru 20 da suka gabata da mudun shinkafa daya bayan da ta koyi sana’ar a jihar Bauchi.

Ta ce:

"Na samu nasarori da dama a sana’ar da suka hada da, ilmantar da ‘ya’yana uku. Daya yana karatu a jami'a; dayan yana makarantar koyon addinin kirista, yayin da na karshe ya yi aure cikin farin ciki.
“Ina godiya ga Allah da ni’imar sa da ya ba ni tsawon shekaru. Sana'ar masa ta kawo min arziki.
“Na gina gida a nan Gombe, wani kuma a Jos kuma ina da filin da ba a gina shi ba, wanda kuma da kudin wannan sana’ar na saya.”

Sirrin samun nasararta

Ta danganta nasarorin da ta samu a wannan sana’ar ga ikon Allah, hakuri, juriya da kuma kyakkyawar al’adar tanadi, kamar yadda ta shaidawa NAN.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Ta shawarci mata da kada su ji tsoron fara kananan sana’o’i, inda ta kara da cewa kananan abubuwa da hakuri da daidaito na iya samar da nasara kawai a jira lokaci.

Dung ta kuma shawarci wadanda suka kammala karatunsu a digiri da su nemi kananan sana’o’i domin su fara da cewa Allah da kuma jajircewarsu a kan sana’ar za su bunkasa rayuwarsu maimakon jiran aikin gwamnati.

Ta yi kira ga gwamnatin jihar da sauran ’yan Najeriya masu kishin kasa da su rika tallafa wa mata a ko yaushe da dabarun da suka dace da jarin fara aiki.

Matashi ya yi farin cikin kammala Digiri bayan shekara 10 ya na fafatawa a ABU Zaria

A wani labarin na daban, wani Bawan Allah mai suna Abba Abubakar Santalee ya bayyana farin cikinsa yayin da ya kammala karatun digirin farko a jami’ar ABU Zaria.

Legit.ng Hausa ta fahimci Abba Abubakar Santalee ya fito ya bayyana wannan abin alheri ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu 2022.

Kara karanta wannan

Ka kawo mana jikoki ko ka bamu N270: Iyaye sun maka dansu a kotu bisa kin haihuwa

Inda farin cikin Pharm. Abba Abubakar Santalee yake shi ne, ya dauki lokaci mai tsawo kafin samun takardar shaidar Digiri a wannan babbar jami’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel