Bikin sauya sheka: Tashin hankali yayin da jiga-jigan PDP 70 suka sauya sheka zuwa APC

Bikin sauya sheka: Tashin hankali yayin da jiga-jigan PDP 70 suka sauya sheka zuwa APC

  • Rahoto ya bayyana cewa, akalla mutane 70 'yan jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Gombe sun sauya sheka
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ganin karuwar sauya sheka a tsakanin 'yan siyasar jihar
  • A rahoton da muka samo, mutanen 70 sun bayyana manufarsu ta komawa APC daga PDP ba tare da wata matsala ba

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, jam’iyyar APC reshen jihar Gombe ta samu karbuwa yayin da ta karbi wasu mutane 70 da suka sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP a karamar hukumar Dukku da ke jihar.

Jiga-jigan wadanda shugabannin jam’iyyar a unguwannin a karamar hukumar ne sun bayyana sauya sheka zuwa APC a karshen mako a lokacin da suka ziyarci gwamnan jihar, Inuwa Yahaya.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Bayan watsi da kujerar da Ganduje ya bashi, Yakasai ya fita daga APC

Jam'iyyar APC ta yi baki a Gombe
Bikin sauya sheka: Tashin hankali j yayin da jiga-jigan PDP 70 suka sauya sheka zuwa APC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Da yake karbarsu, gwamnan wanda shugaban ma’aikatan sa Abubakar Kari ya wakilta ya bayyana jin dadinsu da sauya shekarsu zuwa jam’iyya mai mulki tare da ba su tabbacin cewa za a dauke su tamkar tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar.

Ya ce gwamnatinsa ta mutane ce mai kishin kasa da kyakkyawar manufa ta kawo ci gaba a kofar gidansu, ya kuma yi kira gare su da su kara gamsar da ‘ya’yan jam’iyyun adawa su koma APC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Ina yabawa hangen nesan ku na shiga APC bisa la’akari da ayyukan raya kasa da gwamnatinmu ta aiwatar a yankunan ku. Wannan manuniya ce kun shiga siyasa domin ka zama wakilin jama’arka na gaskiya.
“Gwamnatin Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya a ko da yaushe ta damu ne da jama’a a matakin kasa don haka ya yanke shawarar bayar da kwangilar ayyukan hanyoyin da suka hada Gombe Abba, Kunde har zuwa karamar hukumar Kirfi ta jihar Bauchi."

Kara karanta wannan

Shugabar APC ta mutu a wajen musayar wuta tsakanin ‘Yan bindiga da ‘Yan banga

Tun da farko, tsohon sakataren PDP na gundumar Kunde Liman Abubakar wanda ya yi magana a madadin sauran wadanda suka sauya sheka ya ce sun je ne domin nuna goyon bayansu ga gwamnatin Inuwa.

A cewarsa, mutane 70 da suka sauya sheka sun fito ne daga unguwanni uku a karamar hukumar Dukku da suka hada da Gombe Abba, Zange da Kunde.

Dan majalisar jiha mai ci ya bar PDP, ya koma APC a Gombe

Yayin da 'yan siyasar Gombe ke ci gaba da kaura daga jam'iyyun siyasar da suke zuwa wasu, a yau an tashi da labarin sauya shekar dan majalisa mai wakiltar Nafada ta Kudu, Hon. Adamu A. Musa daga PDP zuwa APC mai mulkin jihar.

A cikin wata wasika da dan majalisar ya rubuta da hannu, kana aka yada a kafar sada zumunta na Facebook, an ga kalaman da ya yi cikin sauki, inda ya ce zamansa a PDP ya kare.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna Al-Makura: Ku bani shugabancin APC na mikar da ita hanya dodar

Abdul No Shaking, daya daga cikin hadiman gwamnan jihar Gombe kan harkokin kafafen yada labarai na zamani, ya yada hoto tare da wasikar barin PDP na Hon. Adamu A Musa.

Wasikar ba ta bayyana wani dalili na barinsa jam'iyyar ba, kana bata bayyana komawarsa APC, sai dai, hadimin gwamnan ya ce tuni dan majalisar ya shigo APC.

Rikicin APC a Zamfara: Magoya Bayan Matawalle a Garinsu Sun Juya Masa Baya, Sun Koma Ɓangaren Marafa

A wani labarin, jiga-jigan jam’iyyar APC daga karamar hukumar Maradun, asalin garinsu Gwamna Bello Matawalle, sun bayyana goyon bayan su ga bangaren jam’iyyar na Sanata Kabiru Garba Marafa, The Punch ta ruwaito.

Jagororin su sun hada da Captain Halilu Haliru mai murabus da kuma tsohon darekta janar na ma’aikatan gwamnatin jihar, Malam Sale ST, wadanda suka yanke shawarar juya wa Matawalle baya akan gaza yi wa jihar aikin a zo a gani.

Kara karanta wannan

PDP ta tausayawa matasa wajen biyan kudin fam din takara, ta rage masu 50% da wasu hukunci 11 da ta zartar

Bangaren da suka juya masa baya sun samu karbuwa zuwa bangaren APC na Sanata Marafa, inda Hon Bello Bakyasuwa ya amshe su hannu bibbiyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel