"Duk na Kere Su": Atiku Ya Kwatanta Farin Jininsa da na Kwankwaso, Tambuwal a Arewa
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Atiku ya yi magana a kan yawan masoya da ya ke da su a siyasar Arewacin Najeriya
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana da mafi girman goyon baya a Arewa fiye da Rabi'u Musa Kwankwaso da Aminu Waziri Tambuwal
- Ya jaddada cewa Arewa na kara hade kai a siyasa kuma hakan na masa amfani sosai yayin da 2027 ke kara matsowa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja –Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yana da karfin goyon bayan siyasa a yankin Arewacin Najeriya fiye da sauran fitattun ‘yan siyasa daga yankin.
Ya bayyana cewa daga cikin waɗanda ya ke ganin ya fi yawan masoya akwai Sanata Rabiu Musa da tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal.

Source: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar Arise News a yammacin ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu na shekarar 2026.
'Ina da masoya sosai a Arewa' - Atiku Abubakar
Jaridar Leadership ta wallafa Atiku Abubakar na cewa duk da yadda Arewa ke kara hade kai a siyasance, tasirinsa a yankin ba kama kafar yaro, domin shi jigo ne a siyasar yankin.
Ya kalubalanci batun kwatanta karfinsa da na sauran ‘yan siyasa na Arewa, yana mai cewa babu wanda ya kai shi yawan kuri’u da kuma tasirin siyasa a yankin.

Source: Facebook
A cewarsa:
“Ku fada min wane dan takara a Arewa ne yake da irin wannan gagarumin goyon baya da nake da shi? Kuna magana ne kan Tambuwal da Kwankwaso da kuma sababbin ‘yan siyasa masu tasowa, amma babu wanda ya kai ni samun kuri’un hadin kai daga yankin.”
Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan
Jigon ADC ya 'gano' halin da APC ke ciki, ya fadi hadin da zai kai Tinubu ƙasa a 2027
"Ina ganin Arewa a yanzu ta fi kasancewa a hade fiye da rabuwar kai. Yankin Arewa ta Tsakiya kuwa yana da nasa salon siyasa mai zaman kansa saboda matsayinsa na tsaka-tsaki.”
Arewa ce ginshikin siyasar Atiku
Atiku ya jaddada cewa yankin Arewa har yanzu shi ne ginshikin karfinsa na siyasa, inda ya yi nuni da yadda ya samu nasara a jihohi da dama na yankin a zaben ƙasa na karshe.
Ya ce:
“Arewa har yanzu ita ce babbar cibiyar goyon bayana. Na lashe jihohi da dama a Arewa a zaben da ya gabata. A Kudu maso Yamma jihohi biyu kawai na samu, kuma ban samu ko guda ba a Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.”
Haka kuma, ya kwatanta yadda karfin siyasa ya rabu a sassa daban-daban na kasar, yana mai cewa kowane yanki na da jagororin da suka fi rinjaye.
Ya ce:
"Kamar yadda Kudu maso Gabas ke karkashin tasirin Peter Obi, haka kuma Kudu maso Kudu ke karkashin tasirin Rotimi Amaechi.”
Duk da haka, Atiku ya amince cewa Kwankwaso na da karfi a jihar Kano, amma ya ce wannan karfi ya takaita ne a yankin guda kuma yana fuskantar rabuwar kai.
A cewarsa:
“Kwankwaso yana da karfi a Kano, shi ya sa ake daukarsa a matsayin jagora a hadakar siyasa. Rashin kuri’un Kano zai iya shafa ta, amma a bangarensa, za ku ga yadda aka raba kuri’u tsakanin sa da tsohon gwamnan jihar.”
Atiku zai hakura da takara bayan 2027
A baya, mun wallafa cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam'iyyar ADC za ta yi amfani da tsarin fitar da dan takara ta hanyar maslaha ko kuma zabe kai tsaye wajen fitar da ɗan takara.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma tabo batun janyewa wani daga cikin 'yan takarar da ke neman tikitin jam'iyyar ADC a babban zaɓe da ke tafe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

