Babbar magana: Jigon siyasar Gombe, Sanata Goje zai koma PDP ranar Laraba mai zuwa

Babbar magana: Jigon siyasar Gombe, Sanata Goje zai koma PDP ranar Laraba mai zuwa

  • Wata majiyar kusa da tsohon gwamnan jihar Gombe ta bayyana yiwuwar shigowar Goje jam'iyyar PDP
  • Ta bayyana cewa, tuni Goje ya shirya komai a hukumance domin shiga jam'iyyar, lamarin da ya biyo bayan rikici tsakanin Goje da Inuwa
  • Goje na daya daga cikin wadanda suke juya akalar siyasar jihar Gombe, kasancewar ya yi gwamna a jihar

Jihar Gombe - A wani mataki na siyasa, tsohon gwamnan jihar Gombe kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Mohammed Danjuma Goje, na iya sauya sheka daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta PDP a ranar Laraba, Afrilu 6.

Wani na hannun daman tsohon gwamnan ne ya shaidawa wakilin jaridar Leadership cewa, an kammala shirye-shiryen shigan Goje PDP a hukumance amma ya ki cewa komai lokacin da aka nemi yayi magana kan shirin sauya shekar tasa.

Kara karanta wannan

Hadimin Sule Lamido da wasu jiga-jigan PDP sun fice daga jam'iyya, sun koma NNPP ta Kwankwaso

Sanata Goje zai shiga PDP gobe Laraba
Babbar magana: Jigon siyasar Gombe, Sanata Goje zai koma PDP ranar Laraba mai zuwa | Hoto: leadership.ng

A cewar na kusa da Goje:

"Ni ba mai magana da yawunsa ba ne amma na san cewa akwai irin wannan shirin a kasa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani jigo a jam’iyyar PDP (wanda ya nemi a sakaya sunansa) ya tabbatar wa jaridar The Guardian cewa:

“Bari na fada muku, kuma na nuna muku cewa siyasa ta sauya a jihar Gombe. Ku zo Sakatariyar mu (PDP) ranar Laraba ku ga yadda Goje ya sauya sheka da magoya bayansa sama da miliyan guda.”

Tushen matsalar da ta sa Goje ka iya sauya sheka zuwa PDP

An dade ana takun saka tsakanin Goje da Gwamna mai ci na jihar Gombe, Inuwa Yahaya wanda ya bijirewa duk wani yunkuri na sulhu tsakaninsu.

Leadership ta ruwaito cewa hedkwatar jam’iyyar APC ta kasa ta yi aiki tukuru a watannin da suka gabata domin sasanta jiga-jigan siyasar biyu, amma abin ya ci tura.

Kara karanta wannan

Saraki, Tambuwal, Mohammed sun kulla yarjejeniya kan wanda zai zama mataimakin shugaban kasa a 2023

A kwanakin baya ne tsohon gwamnan kuma jigo a majalisar dattawa ya yi zargin cewa jam’iyyar APC reshen jihar ta nuna halin ko in kula kan yunkurin sulhu da shugabannin jam’iyyar na kasa suka fara tsakaninsu.

Idan baku manta ba, shigowar Goje a karshen 2021 jihar Gombe ya haifar da rikici tsakanin 'yan tsagin gwamnan Inuwa Yahaya da 'yan tsagin Goje.

Ba mu da labari, amma idan da gaske ne muna tare dashi

Wani shugaban matasa masoya Sanata Danjuma Goje a jihar Gombe, Abdulazeez Alhassan ya zanta da wakilin Legit.ng Hausa, ya kuma shaida masa cewa, ya zuwa yanzu dai basu samu labarin sauya shekar Goje ba a matsayinsu na matasa da ake damawa dasu.

Hakazalika, ya kuma bayyana cewa, ba jam'iyyar Goje ne a gabansu masoya Goje ba face kaunar da suke masa da irin alherinsa.

A kalamansa:

"Bamu ji labarin sauya shekar mai gida Goje ba, amma ba mu da zabi idan ya sauya sheka, muna nan biye dashi.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: PDP ta kara samun cikas, wani babban jigonta ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC

"Goje muke bi ba jam'iyyar da yake bi ba, don haka idan ya sauya sheka zuwa PDP, tabbas muna tare dashi duk inda yake."

Tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya shiga tseren takarar Sanata a 2023

A wani labarin, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, ya bayyana kudirinsa na wakiltar mazaɓar Edo ta arewa a majalisar dattawan Najeriya.

Oshiomhole ya ayyana haka ne a wurin bikin cikarsa shekara 70 a duniya wanda ya gudana a mahaifarsa Iyamho, karamar hukumar Etsako West, jihar Edo, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

A baya shugabannin APC na kananan hukumomi da gundumomi sun roke shi da ya wakilci mazabar a majalisar dattawan kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel