Shirin 2023: Sanatan APC Goje ya raba babura 1000 da keke NAPEP 500 watanni kafin zabe

Shirin 2023: Sanatan APC Goje ya raba babura 1000 da keke NAPEP 500 watanni kafin zabe

  • Sanata Muhammad Danjuma Goje ya baiwa ‘yan mazabarsa a majalisar dattawan Gombe ta tsakiya ababen hawa
  • Goje, tsohon gwamnan jihar Gombe, ya kuma bayyana cewa an dauki matakin rabon ne domin samar da ayyukan yi ga matasa a yankin
  • Sanata Goje, dan majalisar dattijai mai ci, yana shirin komawa majalisar dattawar ne a babban zaben 2023 mai zuwa

Gombe - Tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje ya fara rabon babura masu kafa uku (Keke Napep) 500 da babura 1000 a mazabarsa a gundumar Gombe ta tsakiya.

A cewar Goje, hakan na daga cikin kokarinsa na yaki da talauci tare da karfafawa talakawan mazabar sa da samar musu da aikin yi, kamar yadda Legit.ng ta samo.

Sanatan na jam’iyyar APC, ya kuma bayyana cewa ya dauki matakin ne domin samar da ayyukan yi ga matasa a yankinsa.

Kara karanta wannan

Yaudara da neman goyon baya: Martanin Shehu Sani kan ikirarin Osinbajo na bin sahun Buhari

Goje ya yi rabon ababen hawa
Shirin 2023: Sanatan APC Goje ya raba babura 1000 da keke NAPEP 500 watanni kafin zabe | Hoto: Goje media team
Asali: Facebook

Sanatan wanda tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Gombe Abubakar Sadeeq Kurba ya wakilta a yayin rabon baburan a Gombe, ya bayyana cewa tallafin ya samo asali ne daga kokarinsa na tallafawa matasa da mata a mazabar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

“Taimakon babura guda 1000 da babura 500 da suka shigo a yau na daya daga cikin dubunnan kyaututtuka da muke yi wa al’ummar Gombe ta tsakiya.”

Goje ya kara da cewa kawo yanzu sama da mutane 5000 na mazabar sa ne suka ci gajiyar shirin nasa wanda ya hada da shirin rage yunwa daga kudaden da aka raba don amfani da su a matsayin jari da kuma kayan abinci da aka raba a farkon wannan watan na Ramadanan.

Ya kara da cewa:

"An ba wa dukkan kayayyakin ne gaba dayansu kyauta ga wadanda suka ci gajiyar shirin, ba lamuni ba ne ko kuma wani shiri daga kowa, kuma babu wanda ake sa ran za a salla ko ya biya wani."

Kara karanta wannan

Bala Mohammed: Buhari ya yi rugu-rugu da Najeriya amma ni zan gyara ta

Wadanda suka ci gajiyar shirin sun tofa albarkacin bakinsu

Daya daga cikin wadanda suka ci moriyar babur din mai suna Rose Danjuma ta bayyana cewa farin cikinta ba zai misaltu ba, inda ta bayyana cewa farin cikin karshe da iyalanta suka ji shine lokacin da Sanata Goje ke rike da mukamin gwamnan jihar Gombe.

Ta fadawa manema labarai cewa:

“Sanata Muhammad Danjuma Goje jarumi ne na gaskiya a fagen yaki da talauci a tsakanin al’ummarmu.

Ga Muhammad Sarkiwa Umar mai unguwar Kombani dake karamar hukumar Akko, babur din da aka ba shi zai kawo masa dauki tare da bunkasa sana’arsa ta noma.

Yace:

''Babu wata kalma da zan iya amfani da ita don nuna farin cikina da wannan kyauta, amma abu daya da na tabbatar shi ne cewa lallai Goje ya taimake ni kuma Allah Ya saka masa da alheri.''

Wakilin Legit.ng Hausa ya tambayi daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin, Garba Saleh, wani mazaunin Bomala, kan tsarin da aka bi wajen ba da kyautar, sai ya ce:

Kara karanta wannan

Idan dai cancanta ake bi’da shugabancin Najeriya sai Amaechi – Sarkin Dutse

"Ni dai Allah ya tsaga da rabo na, kuma sunana aka dauka aka tafi dashi, sannan aka ce za a yi bikin ba da mashin din, sai gashi ina ciki. Alhamdulillahi Allah ya sakawa Goje, ya kuma ba shi abin da yake nema."

N30,000: Sanatan APC Goje ya baiwa matasa da mata sama da 2,000 tallafin dogaro da kai

A wani labarin, matasa da mata 2,200 a Gombe ne Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa ta kasa, Sanata Danjuma Goje ya ba tallafin sana'a.

Legit.ng ta samo cewa, Goje, wanda tsohon gwamnan jihar Gombe ne ya raba musu makudan kudade a matsayin jarin fara kasuwancin da suka iya a ranar Litinin, 29 ga watan Maris.

Daga cikin mutane 2,200 da suka ci gajiyar shirin karfafawar ta Sanata Goje, 1000 matasa maza ne yayin da 1,200 kuma mata ne, wadanda dukkansu sun fito ne daga kananan hukumomin Yamaltu-Deba da Akko.

Kara karanta wannan

Buhari ya gaza, kuma bai shirya magance matsalar rashin tsaro ba, inji Sanata mai ci

Asali: Legit.ng

Online view pixel