Dankwambo ya dawo Gombe bayan shekaru 3, ya ce har yanzu PDP ce burin talaka

Dankwambo ya dawo Gombe bayan shekaru 3, ya ce har yanzu PDP ce burin talaka

  • Gabannin zaben 2023, tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya dawo jiharsa bayan shekaru uku da barinsa mulki
  • Dankwambo ya sha alwashin dawo da PDP karagar mulki a jihar Gombe domin a cewarsa ita ce burin mutanen jihar
  • Ya ce zuwa yanzu dai ba a nemi ya tsaya takarar kowace kujera ba gabannin babban zaben 2023

Gombe - Shekaru uku bayan saukarsa daga kujerar shugabanci, tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya dawo jihar tare da alkawarin dawo da jam’iyyar PDP kan mulki a jihar.

Dankwambo wanda ya samu tarba daga dandazon jama’a a filin jirgin sama na Gombe zuwa satariyar PDP a jihar, ya ce gwamnatin APC mai mulki na cin zarafi da razana mutanen jihar.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a gidansa kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaro, billahi lazi zamu dauko Sojin haya: El-Rufa'i ya fusata

Dankwambo ya dawo Gombe bayan shekaru 3, ya ce har yanzu PDP ce burin talaka
Dankwambo ya dawo Gombe bayan shekaru 3, ya ce har yanzu PDP ce burin talaka Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gaba daya abubuwa ba sauki; abubuwa sun yi wahala matuka. Mutane na ciki tsoro da razana, amma har yanzu mutanen Gombe basu yanke kauna ba kuma ina so su ci gaba da rike wannan fatan.
“Ina so in mika godiyata ta musamman ga mutanen da suka fito kwansu da kwarkwatansu domin yi mini barka da dawowa jihar daga Abuja a filin jirgin sama. Ban gayyaci kowa ba; Ban sanar da kowa cewa ina zuwa ba. Ina so ne kawai in zo in yi gaisuwa ga jama’ata, in jajanta wa wasu wurare, da kumayiwa jama’ar Gombe fatan alheri.”

Tsohon gwamnan ya kuma ce ba zai iya yin wani jawabi kan halin da Gombe ke ciki bayan barinsa gwamnati ba, inda ya kara da cewar yana bukatar tattaunawa da mutanen Gombe kafin y ace komai kan halin da jihar ke ciki.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindigan sun kai hari gidan Kwamishinan jiha, sun tada bama-bamai

Ya ce:

“Yaya Gombe take kuma menene banbancin a shekaru uku da suka gabata? A yan kwanaki masu zuwa, zan fahimci yadda Gombe take. Ko akwai ci gaban a shekaru uku da suka gabata – ko akwai ci gaba a bangaren dan adam, ci gaba a bangaren talauci, jin dadin jama'a, tsaro da sauran alamomi? Kafin in tafi, idan kuka zo irin haka, zan gaya muku bambanci.”

Kan makomar siyasarsa, Dankwambo ya ce a yanzu, ba a gayyace shi domin ya fito takarar komai ba, duk da cewar ya taba takarar kujerar shugaban kasa, rahoton The Eagle online.

Ban sani ba ko za a yi zaben 2023 domin Allah bai sanar dani ba tukuna – Shahararren malamin addini

A wani labarin, Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God, Fasto Enoch Adeboye, ya ce har yanzu bai sani ba tukuna ko za a yi babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

N30,000: Sanatan APC Goje ya baiwa matasa da mata sama da 2,000 tallafin dogaro da kai

Malamin addinin mai shekaru 80 a duniya ya ce Allah bai fada masa ko za a yi wani zabe ba a shekara mai zuwa.

Ya ce Allah ya yi masa magana game da zaben 2019 fiye da shekara guda kafin zaben amma a wannan karon bai aikata hakan ba a kan zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel